AIKIN HANYA: Al’ummar Ladduga Sun Yabawa Kamfanin FARMTRAC

0
493

Rabo Haladu Daga Kaduna

Bisa aiwatar da aiki mai inganci da nagarta da kamfanin Kwangilar aikin hanya na FARMTRAC yakeyi a karamar hukumar Kachia a jihar Kaduna, al’ummomin yankin sun Yaba da kokarin kamfanin da gwamnatin jihar Kaduna bisa aiwatar da ayyukan hanya a yankin.

Al’ummomin sun bayyana cewa aikin hanyar kauyen Ludduga da kamfanin yake yi zai taimaka wajen rage musu matsalar jigilar amfanin gona da bunkasa harkokin kasuwanci a yankin.

Wasu mazauna Yankin da suka zanta da manema labarai sun bayyana gamsuwar su dangane da irin aikin da kamfanin Farmtrac yake yi inda suka ce kamfanin ya cancanci yabo bisa irin nagartaccen aiki da suka yi.
Sun ce kamfanin Farmtrac ya fidda gwamnatin jihar Kaduna kunya wajen aiwatar da aikin da al’ummomin zasu Dade suna amfana dashi musamman ganin cewa kauyen Ladduga ya Dade Yana Fama da rashin hanya mai kyau wanda hakan yake haifar musu da matsaloli Masu yawan gaske. A cewar su yanzu gashi gwamnatin Kaduna ta Bawa Dan Kwangila mai kishi alhakin yin titin.
Mallam Ja’afar Salihu , shugaban matasa kungiyar fulani ta ,Miyetti Allah na karamar hukumar Kachia wanda kuma shine Dagacin kauyen Laduga, yace ” muna rayuwa a nan garin sama da shekaru 30 ba tare da hanyar mota ba amma gashi yanzu an fara aiwatar da aikin hanyar duk da cewa har yanzu ba’a kammala aikin ba amma ya zama dole mu Jinjinawa gwamna El-Rufai na bada Kwangilar hanyar duk da cewa a baya mun Riga mun fidda tsammani akan gwamnatin”.
Shima a nasa Jawabin, Alhaji Rabo Yusuf, Majidadi wanda kuma shine Sarduana Laduga, yace kamfanin Farmtrac ya nuna zai aiwatar da aiki mai inganci da nagarta musamman ganin yadda ya dauko aikin hanya wanda bai Sani ba zai dauka cewa aikin gwamnatin tarayya ne Musamman aikin gada da kamfanin yayi akan hanyar”
Shima, Marafan Laduga ,Alhaji  Shaibu Usman, ya bayyana cewa a shekarun baya muna kwashe kwanaki Kamin mu fito bakin titin jirgin kasa amma yanzu cikin mintuna 10 zuwa 15 mun iso bakin hanya”
“Tunda nake ban taba ganin aikin hanya mai inganci da nagarta ba kamar wanda yanzu akeyi a kauyen Ludduga ba wanda kamfanin na gida yake yi wanda Idan ka gani zaka zaci na kamfanin kasar waje ne yake yi” inji shi.
Tsohon shugaban Masu rinjiye na Majalisar Dokokin jihar Kaduna Devid Umar Gurara, yace ya zama wajibi su Jinjinawa gwamna El-Rufai da kamfanin Farmtrac bisa nagartaccen aiki da suka yi a karamar hukumar Kachia Yana mai cewa ” ni Dan jam’iyyar PDP amma na gamsu da gwamnatin El-Rufai bisa ayyukan Raya kasa da yakeyi haka kuma ya Bawa kamfanin Farmtrac Kwangilar gudanar da aikin saboda babu abin da zamu cewa gwamnatin El-Rufai da kamfanin Farmtrac Sai godiya.Injinjya Sadiq Tare Da Gwamna El-Rufai

A nasa Jawabin Shugaban kamfanin Farmtrac Injiniya Sadiq Abukakar, ya godewa gwamnatin jihar Kaduna daya ba kamfanin shi damar aiwatar da aikin hanyar.
Injiniya Sadiq, ya ce manufar kamfanin Farmtrac shine samar da kyakkyawar aiki wanda jama’a zasu amfana da shi da kuma Gina kamfanin Kwangilar hanyar mai dorewa wanda zaiyi gogayya da na kasashen waje ta kowanne bangaren.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here