Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutum 16 A Abuja Da Neja

0
401

Daga Usman Nasidi.

RAHOTANNI sun tabbatar da mutuwar mutum shida yayin da ake nemi mutane biyar aka rasa a ranar Asabar biyo bayan saukar wani ruwan sama na mamako a garin Suleja na jihar Neja.

Majiyarmu ta ba da rahoton cewa ruwan saman da ya sauka tamkar da bakin kwarya da sanyin safiya ya haifar da ambaliyar ruwa a mafi akasarin yankunan garin Suleja.

Darakta Janar na Hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar Neja, Ibrahim Ahmed Inga, shi ne ya ba da tabbacin hakan da cewa an tsinto gawawwaki mutum shida da ruwa ya tafi da su.

Yayin tattaro wannan rahoto, ya ce an nemi mutane 11 an rasa, amma yayin da aka tsamo gawar mutum shida, a yanzu mutum biyar ne kawai ba a san halin da suke ciki ba walau a raye ko a mace.

Ya ba da tabbacin cewa, ambaliyar ruwan ta fi muni a wasu yankuna biyu na jihar da suka hadar da; Unguwar Gwari da POP.

Haka zalika wata mata mai dauke da juna biyu tare da ‘ya;yanta hudu, na cikin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwan da ta auku a yankin Gwagwalada da ke Abuja, babban birnin Najeriya.

Rahotanni sun bayyana cewa, matar ‘yar shekaru 27 mai suna Habiba Hamid, ta riga mu gidan gaskiya tare da ‘ya’yanta; Ladifa, Rahama, Abdullatif da kuma Rabi’u.

An tafka ruwan sama na mamako da ya fara sauka tun da misalin karfe 2.00 na ranar Juma’a da daddare wanda ya ci gidaje da dama da suka datsi magudanan ruwa a unguwar mayanka da ke garin Gwagwalada ta birnin Abuja

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here