An Kama Ɗan Fasto Da Wasu Mutum 5 Da Ake Zargi Da Yi Wa ‘Yar Shekara 12 Fyaɗe

0
840

Daga Usman Nasidi.

YARON wani Fasto da wasu mutane biyar da ake zargi da aikata fyade, a yanzu haka an garkame su a dakin ajiye masu laifi na ofishin rundunar ‘yan sandan jihar Akwa Ibom da ke birnin Uyo.

Jami’in hulda da Jama’a rundunar ‘yan sanda na jihar, CSP N-Nudam Fredrick, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a karshen mako.

Ya ce duk mutane shidan da ake zargi sun amsa laifin biyan bukatarsu ta sha’awa da budurwa matashiya mai kananan shekaru.

Rahotanni sun bayyana cewa ababen zargin sun shiga hannu ne bayan an shigar da korafi ga ofishin ‘yan sandan kan ta’asar da suka aikata.

A cewar CSP Fredrick, kwamishinan ‘yan sanda na jihar Edgar Imohimi, ya lashi takobin cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kwato hakkin matan da aka ketawa haddi.

Ya nakalto kwamishinan ‘yan sandan yana shawartar duk wadanda suka fada tarkon fyade , a kan kada su ji tsoro ko kunyar shigar da kara domin a nema musu hakki.

CP Imohimi ya kuma yabawa hukumar shari’a ta jihar dangane da yadda ta ke gaggauta zartar da hukuncin kan miyagun mutane masu ta’adar fyade.

Ya kara da cewa, masu irin wannan mugun hali ba za su taba samun wani sukuni ko wata nutsuwa ba matukar sun shiga hannu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here