An Kashe Mutune 9 A Wani Harin Da Aka Sake Kai Wa Al’ummar Zipkak A Kaduna

0
244

 Usman Nasidi, Daga Kaduna.

RAHOTANNI sun kawo cewa an kashe mutane tara a wani hari da aka kai kan al’umman Zipkak da ke karamar hukumar Jama’a na jihar Kaduna.

Yankin Jama’a na daga cikin kananan hukumomin da gwamnatin Kaduna ta sanya dokar kulle na sa’o’i 24 saboda rashin tsaro amma duk da haka aka ci gaba da kai hare-hare.

An tattaro cewa ‘yan bindiga sun far ma kauyen, wanda ya ke kimanin rabin kilomita daga Kafanchan, hedkwatar karamar hukumar Jama’a, da misalin karfe 6:30 na yammacin ranar Juma’a.

Gideon Mutum , wani mazaunin yankin, ya ce kimanin kwanaki uku da suka gabata, an yada jita-jitan cewa za a kawo hari amma ba a tsaurara matakan tsaro ba.

Ya bayyana cewa Shama Ishaya, wani fasto na cocin Evangelical Church Winning All (ECWA), na daga cikin wadanda aka kashe a sabon harin.

Ya ce wasu 11 sun ji raunuka daga harbe-harben bindiga yayinda aka kona gidaje biyar.

Ya kara da cewar shida daga cikin wadanda suka ji rauni na a cikin mawuyacin hali a asibitin koyarwa na jami’ar Jos (JUTH), jihar Plateau, inda suke jinya.

“Karfin gwiwar da gwamnati ke bamu a koda yaushe shine cewa muna da tawagar tsaron hadin gwiwa a nan Kafanchan, amma duk mun san cewa bamu da isassun mutane kuma babu kayayyakin bukata na tsaro,” in ji shi.

“A jiya, babu wani kokari da sojoji suka yi a lokacin harin da aka kai garin amma an shammace su saboda ‘yan ta’addan sun zo sun aiwatar da kashe-kashen a dan kankanin lokaci sannan suka tafi ba tare da jami’an tsaro sun cafke su ba.

“Dokar kulle ba zai yi maganin matsalar ba, maimakon hakan zai kara yawan kashe-kashen, duba ga abunda muka fuskanta a sauran garuruwan da aka sanya dokar kulle na sa’o’i 24 sama da wata daya.

“Mun ga yadda ake kashe mutane duk da dokar kulle, maimakon haka ma ya farfafa masu gwiwa tare da ba makiyaya damar kai farmaki garuruwa da kuma kashe mutane yadda suke so.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here