Ba Da Kwangiloli Ba Bisa Ka’ida Ba Na Cikin Dalilaina Na Barin PDP – Dogara

  0
  399

  Rahoton Z A Sada

  TSOHON kakakin majalisar wakilan Najeriya ya ce bayar da kwangiloli ba bisa ka’ida ba da gwamnatin jiharsa ta Bauchi ke yi na cikin manyan dalilan da suka sanya shi dungurar da shahadar jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyarsa ta asali APC.

  Ya kuma bayyana damuwa kan rashin biyan ma’aikata albashi a kan lokaci, da kuma rashin gudanar da zabukan kananan hukumomi cikin wata shida na farko, kamar yadda gwamna Bala Muhammad ya yi alkawarin zai yi.

  Gwamnan Bauchi Bala Muhammad da tsohon shugaban majalisar wakilan Najeriya Yakubu Dogara a lokacin yakin neman zaben 2019

  ”Gwamnati ta ciyo bashi na Naira biliyan hudu, daga baya aka gano kudin a asusun wani kamfani mai zaman kansa, duk da cewa an ranto su ne da sunan jihar Bauchi, sannan ana bayar da kwangiloli ba bisa ka’ida ba, baya ga ninka kudin da ake yi yadda aka ga dama ba tare da bin ka’idojin doka ba.”

  Yakubu Dogara ya bayyana haka ne ta bakin mai magana da yawunsa. Turaki Hassan yayin zantawa da BBC, inda ya ce ba gaskiya ba ne zargin da wasu ke yi cewa ya sauya sheka ne saboda hankoron samun wata dama a APC.

  Dogara ya kuma ce wata matsalar da ya gani a jagorancin gwamnatin PDPn Bauchi ita ce rashin girmama manya, da sarakuna da gwamnan ke yi, saɓanin alkawuran da ya yi a baya na cewa zai rika daraja su.

  Wadannnan dalilai da kuma karin wasu ne suka sanya Yakubu Dogara yaga cewa ba zai iya ci gaba da zama a inuwa daya da gwamna Bala Muhammad ba, in ji Turaki Hassan, mai magana da yawun dogara.

  Shugaba Buhari tare da Yakubu Dogara bayan sake komawa APC

  Mai magana da yawun kakakin tsohon shugaban majalisar wakilan Najeriyar ya musanta zargin cewa Dogara, na da wani ra’ayi neman sake zama shugaban majalisar wakilan Najeriya ko ma yin takarar gwamna a zabe mai zuwa.

  ”Ka fada wa kowa, Dogara ba shi da tunanin yin takarar gwamnan Bauchi, inda yana son ya yi takara ai da ya yi a 2019” In ji shi.

  Ya kuma kara da cewa sun yi iya kokari domin jawo hankalin gwamnan dangane da wadannan matsaloli da suke gani ana samu a Bauchi amma bai yi komai a kai ba.

  A cewarsa, manya da dama sun yi ta kokarin shiga tsakani don warware rashin jituwar da ake samu tsakanin yan siyasar, amma lamarin ya ci tura.

  Shugaban jam’iyyar APC na riko, kuma gwamnan Yobe Mai Mala Buni ne ya sanar da komawar Dogara APC, jim kadan bayan wata ganawa da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

  Mai taimaka wa shugaban kasar kan harkokin watsa labarai Femi Adesina, ya wallafa hotunan yadda ganawar ta kasance a shafukansa na sada zumunta.

  Rabon da a ga shugaba Buhari da Yakubu Dogara tun lokacin da yake kan matsayin shugaban majalisar wakilan Najeriya kafin ya sauka.

  A iya cewa a yanzu Dogara ya yi dawayya ne zuwa tsohon gidan sa, domin tun lokacin da aka kafa APC yake cikin ta, kafin ya fice ya koma PDP a shekarar 2018.

  Yanzu haka dan majalisar wakilai ne da ke wakiltar mazabun Bogoro da Dass, da kuma afawa Balewa, dukkanin su a jihar Bauchi.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here

  %d bloggers like this: