Inganta Aikin Noma Ne Babban Rufin Asirin Najeriya-Farfesa Dadari

  0
  493
  Farfesa Salihu Adamu Dadari,,

  Isah Ahmed Daga Jos

  FARFESA Salihu Adamu Dadari malami ne,  a sashen bincike da koyar da dabarun  noma  na Jami’ar Ahmadu Bello, da ke Zariya. A wanann tattaunawa da ya yi da wakilinmu, ya bayyana cewa inganta aikin noma ne babban rufin asirin Najeriya. Har’ila yau ya bayyana cewa  hana shigo da masara da gwamnatin Buhari tayi,  wata babbar nasara ce, ga gwamnatin. Ga yadda tattaunawar ta kasance:-

  GTK: A matsayinka na masani kan harkokin noma, mene ne za ka ce kan da matakin da gwamnati tarayya ta dauka, na hana shigo da masara daga waje?

  Farfesa Dadari: Wannan mataki da gwamnatin tarayya ta dauka na hana shigo da masara daga waje, tuntuni ya kamata ta dauka. A  shekaru biyu da suka gabata,  kungiyar manoman masara ta Najeriya wadda ina ciki,  domin nine bai basu shawara. Mun kalubalanci shigo da masara da ake yi daga wajen Najeriya.

  Don haka muka rubuta takarda  zuwa ga shugaban kasa, ta hanun gwamnan Jihar Kaduna, aka kaiwa shugaban kasar.

  Nan take aka kiramu taro da  ma’aikatar gona da kungiyar masu kiwon kajin, muka kabulanci wannan  shigo da masara daga waje da ake yi.

  Domin  a shekara ta 2018 kungiyar masu kiwon kaji sun higo da masara tan dubu 300, suna kalubalantar kasuwancin masara a Najeriya. A wajen wannan taro, masu kiwon kajin suka bada kai, bori ya hau.

  Don haka a wajen wannan taro, shugaban kasa ya ce kada a sake shigo da masara daga waje.

  Saboda haka wannan mataki da gwamnatin tarayya ta dauka, na hana shigo da masara  ya yi daidai, domin Najeriya tana noma masara sama da tan miliyan 27,  a duk shekara.

  Kuma bukatar al’ummar Najeriya da kaji na masara, gabaki daya bai fi tan miliyan 13, zuwa tan miliyan 15 ba. Kaga muna da rararar masara a Najeriya.  Idan ka lura wannan rarara ce  ‘yan kasuwa  suke dauka  suna kaiwa kasashen Nijar da Katano da kamaru da sauran kasashen da suke bukata.

  Don haka abin muke fada shi ne, tun da zamu iya noma wannan masara a nan Najeriya, mun gode da daukar wannan  mataki da gwamnatin Buhari ta yi na hana shigo da masara daga waje. Domin gwamnatin  ta baiwa manoma damar su noma abin da suke so, kuma kasuwar duniya zata sayi abin da suka noma, banda wanda zamu yi amfani da shi a Najeriya.

  Saboda haka martabar Najeriya zata dawo kuma  darajar kudinmu za ta farfado. Domin idan kasa tana sayen kaya a waje kudinta, take lalatawa.

  Don haka hana shigo da masara babbar nasara ce ga gwamnatin Buhari.

  GTK: Mene ne kake ganin ya sanya masu gidajen kaji na kudancin kasar nan, suka fi son su shigo da marasa daga waje, maimakon su sayi ta gida?

  Farfesa Dadari: Abin da yasa ka san dan Najeriya da son araha. Ai masarar da suke shigowa da ita daga waje, masarar da ta riga ta dade ne a ajiye. Don haka irin wadannan mutane suke zuwa su dan bada wani abu, a basu su dauko su kawo Najeriya.

  Don haka saboda arahar da suke samu ne, ya sanya suke zuwa su sayo irin wannan masara wadda bata da amfani a wajen turawan, domin zubar da irin wannan masara suke yi, domin ta riga ta gama lalacewa a wajensu.

  GTK: Kamar wace  illa ce kake ganin shigo da masarar nan ya jawowa manoman masara a Najeriya?

  Farfesa Dadari: Gaskiya ilolin suna da yawa, domin  manoma sun yi ta tafka asara, sakamakon shigo da masara daga waje, domin masarar bata daraja. A baya buhun masara baya sayen buhun taki, dole  sai manomi ya yi ciko. Manomin da ada yake noma buhun masara 500, saboda   faduwar da yake yi ya koma   yana noma buhun masara 50.

  GTK: Wannan irin cigaba ne kake ganin daukar wannan mataki  zai kawo wa manoman masara a Najeriya?

  Farfesa Dadari: Babu shakka daukar wannan mataki zai bunkasa noman masara a Najeriya. Kuma manoma za su amfana  ta fannoni daban daban. Manoma zasu sami walwala, su biya ‘yayan kudin makaranta cikin kwanciyar hankali. Kuma wasu za su gina gidaje, wasu za su sami jarin da zasu rika yin safarar masarar, suna kaiwa wurare daban daban.

  Babu shakka inganta noma, shi ne rufin asirin Najeriya da al’ummar Najeriya baki daya.

  Yanzu da bamu yi noma ba, a shekarar da ta gabata,  ina zamu  sa kanmu sakamakon annobar Kurona nan, da ta addabi duniya.

  GTK: Wanne sako ne kake da shi zuwa ga gwamnati da manoman Najeriya?

  Farfesa Dadari: Sakona ga gwamnati shi ne ya kamata gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi su hada kai su taimakawa manoma, su basu dukkan  kayan aikin noma da suke bukata, kan farashi mai rahusa.

  A  kullum kasashen da suka cigaba suna tallafawa fannin noma, domin fannin noma shi ne na daya, a rayuwar duniya. Domin sai mutum yaci abinci, sannan zai yi walwala.

  Haka kuma sakona ga manoman Najeriya shi ne su cigaba da wannan aiki na noma da  suke yi. Kuma su  yiwa Allah godiya da addu’ar samun damina mai albarka.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here