Sojojin Najeriya Sun Tarwatsa Sabon Sansanin ‘Yan Bindiga A Zamfara

0
543

Rahoton Z A Sada

WASU hare-hare da dakarun sojan sama na Najeriya suka kai ya yi sanadiyyar tarwatsa wani sansanin ‘yan fashi a Jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin ƙasar, a cewar hedikwatar tsaron Najeriya.

Sanarwar da hedikwatar tsaron ta wallafa a yau Asabar ta ce dakarun rundunar musamman ta Operation Hadarin Daji sun kai harin ne a Dajin Doumborou ranar Juma’a bayan sun samu wasu bayanan sirri.

Kazalika ta wallafa wani bidiyo a shafinta na Twitter, inda ta ce na harin ne.

“Harin da rundunar Operation Hadarin Daji ta kai ya haifar da kyakkyawan sakamako ta hanyar tarwatsa sabon sansanin ‘yan fashi ƙarƙashin jagorancin ‘Dangote,'” in ji sanarwar.

Sai dai rundunar ba ta bayyana adadin waɗanda ta kashe ba ko kuma suka ji rauni daga cikin ‘yan fashin, haka ma ba ta bayyana ko an samu rasa rai daga ɓangaren nata dakarun ba.

Wannan hari na ɗaya daga cikin waɗanda rundunar ta sha ikirarin kai wa ‘yan fashin, waɗanda suka kashe mutane da dama tare da hana mutanen yankin jihohin Katsina da Zamfara da Sokoto.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here