Ya Kashe Kansa Da Wuka Kan Budurwarsa Za Ta Auri Wani

0
431

Daga Usman Nasidi.

WANI yaro Matashi mai shekaru 25 dan asalin jihar Kano mai suna Ashiru Musa Danrimi, ya kashe kansa ta hanyar sokawa cikinsa wuka a jihar Kano.

An gano cewa matashin ya aikata hakan ne bayan budurwarsa da suka zuba soyayya za ta aura wani mutum da ba shi ba.

Kamar yadda bincike ya bayyana, mamacin dan asalin gundumar Kadawa ne da ke karamar hukumar Ungogo ta jihar Kano.

Hankalinsa ya tashi kuma ya yi matukar harzuka bayan da ya gano cewa budurwasa mai suna Ummi Muhammad ta yanke hukuncin auran wani mutum daban.

Bincike ya nuna cewa, ya mayar da hankali ba kadan ba a kan soyayyarsu saboda ya sadaukar da kudinsa, aljihunsa da lokacinsa.
An zargi cewa ya soka wa kansa wuka bayan samun wannan labarin.

A yayin tabbatar da aukuwar lamarin, Jami’in hulda da Jama’a na rundunar ‘yan sanda jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce ‘yan sanda sun gaggauta mika shi asibitin kwararru na Murtala da ke Kano inda aka tabbatar da mutuwarsa.

Ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Habu Sani, ya umarci sake bincike mai tsanani kuma gamsasshe a kan mummunan lamarin.

Makwabtan mamacin sun bayyana alhininsu da mamaki a kan aukuwar lamarin, domin kuwa sun san irin soyayyar da ke tsakanin masoyan. Basu taba tsammanin za ta kare a hakan ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here