‘Yan Sanda Sun Bayyana Sakamakon Binciken Mawaki D’Banj

0
278

Daga Usman Nasidi.

RUNDUNAR ‘yan sandan Najeriya sun wanke shararren Mawakin nan wanda aka sani da D’Banj daga zargin da wata Seyitan Babatayo ta yi masa na yi mata fyade.

A wani jawabi da ‘yan sanda su ka fitar ta bakin DCP Umar Sanda a madadin mataimakin sufeta janar na kasa wanda ke lura da binciken laifuffuka, an yi fatali da wannan zargi.

Rahotanni sun bayyana cewa, ofishin FCID na ‘yan sandan ya na cewa babu hujjar da ke nuna Tauraron ya yi lalata da Seyitan Babatayo da karfin tsiya.

Sanarwar ta bayyana cewa, Miss Seyitan Babatayo ta jefi D’Banj da zargin yi ma ta fyade da kokarin yi wa maganar rufa-rufa.

Ko da cewa Seyitan ta yi wasa a wannan otel, jami’an ‘yan sanda sun ce babu abin da zai nuna Oladapo Daniel Oyebanjo ya yi lalata da ita, don haka aka kashe maganar.

DCP Sanda ya ce bincike ya nuna babu gaskiya a korafin da Seyitan Babatayo ta yi na cewa Oladapo Daniel Oyebanjo watau D’Banj ya yi amfani da ita ba tare da iznin ta ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here