Za A Ci Gaba Da Jigilar Almajirai Zuwa Jihohinsu – Gwamnonin Arewa

0
223

Daga Usman Nasidi.

RAHOTANNI daga majiya mai tushe na bayyana cewa gwamnoni 19 na yankin jihohin Arewacin Najeriya sun shirya sake ci gaba da maida Almajirai zuwa garuruwansu na asali.

Rahoton ya bayyana cewa jagoran kungiyar gwamnonin jihohin Arewa, kuma sakatarenn gwamnatin jihar Filato, Danladi Atu ya yi wannan bayani a wata hira da aka yi da shi.

Atu ya ce: “Ba mu kammala dauke Almajirai a yankin ba. Gwamnonin Arewa za su zauna kwanan nan, su sa ranar da za a cigaba da maida Almajiran inda su ke fito.”

Danladi Atu ya ke cewa “Amma wannan zai kasance kusan zuwa bayan Sallah.”

A cewar jagoran na NGF, akalla Almajirai 11, 000 aka maida gidajen da aka haife su a jihohin Arewa a lokacin da annobar COVID-19 ta soma aukuwa.

Idan ba za ku manta ba, annobar COVID-19 ta fara kamari ne a Najeriya a watan Mayu. Fiye da watanni biyu kenan ana fama da Coronavirus a kasar nan.

Mista Danladi Atu ya ce a baya gwamnonin yankin sun rika maida almjarai, amma yanzu an dakatar da wannan lamari ne domin bin umarnin shugaban kasa.

Kwanakin baya sakataren gwamnatn tarayya kuma shugaban kwamitin yaki da COVID-19 ya haramtawa gwamnonin Arewa yawo da almajrai daga wuri zuwa wuri.

Yanzu da kwamitin PTF ya dakatar wannan doka, za a koma aikin da aka faro na maida Almajran zuwa kauyuka da garuruwan da iyayensu su ke inji Atu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here