Ba Zan Yafe Wa Wanda Ya Yi Min Kazafi Ba – El-Rufai

0
308
Rabo Haladu Daga Kaduna
GWAMNAN jihar Kaduna  Nasir El-Rufa’i, ya yi wa malaman da suka zarge shi da hana jama’a yin sallah ‘Allah-Ya-isa’.
Gwamnan ya bar malaman da Allah ne a jawabin da ya yi ga ‘yan jihar tasa da yammacin Talata.
A cewarsa “Ko a Makka ba za a yi sallar Idi ba, amma mu a nan malamai sun hau mumbari suna cewa mun hana sallah. Kuma sun sani. Saboda haka Allah ya isa. Na yafe wa duk wanda ya zage ni, amma ba zan yafe wa duk wanda ya zarge ni ba.
Sabanin wasu jihohi, Gwamna Elrufa’i ya ce kowa ya yi sallar idi da Juma’a a gida domin hana bazuwar cutar korona da ke yi wa duniya barazana.
Har wa yau, gwamnan ya zargi jami’an tsaro da ‘cin amana’ inda ya ce jami’an tsaro na karbar na goro domin barin jama’a su shiga Kaduna.
Gwamna Elrufa’i dai bai fadi lokacin da ake sa ran bude jihar ba, inda mataimakiyarsa ta ce har yanzu ba su gamsu da yanayin da cutar take a jihar ba ballantana su bude jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here