Isah Ahmed Daga Jos
TAWAGAR shugabannin kungiyar hada kan kasa ta Peace Corps [NUPENC] ta kai wa Limamin masallacin gidajen ‘yan majalisar tarayya da ke Abuja, kuma Kwamandan Hisba na Abuja, Imam Ibrahim Auwal Usama, ziyarar neman goyan baya. Tawagar shugabannin kungiyar ta kai wannan ziraya ce, a ofishin Kwamandan da ke Abuja.
Da yake jawabi a wajen Kwamandan kungiyar na kasa, Dokta Chinedu S. Nneji ya bayyana cewa sun kawo wannan ziyara ce domin neman goyan baya tare da bayyana manufofin kungiyar.
Ya ce ganin limamin yana daya daga cikin limaman babban birnin tarayya Abuja, kuma Kwamandan Hisba na Abuja suka kawo mana wannan ziyara, don neman goyan baya.
Ya ce kungiyar ta fuskanci kalubale na maganar kabilanci da bangaranci, domin wasu suna kallon kungiyar, kamar wata kungiya ce ta wani addini daban.
Kwamandan ya yi bayanin cewa wannan kungiya babu ruwanta da maganar banbancin addini ko kabila, don haka kowanne dan Najeriya yana da dama ya zo ya shiga cikinta.
‘’Muna bai wa Imam tabbacin cewa za mu hada hannu da shi, don ganin mun yi aiki tare, don haka muna rokon ku taimaka wajen ganin majalisar tarayya ta amince da kudurin da aka gabatar mata, kan kafa wannan kungiya’’.
A nasa jawabin Limamin masallacin gidajen ‘yan majalisar tarayya da ke Abuja, kuma Kwamandan Hisba na Abuja Imam Ibrahim Awwal [Usama] ya bayyana matukar farin cikinsa, kan wannan ziyara da kungiyar ta kawo masa.
Ya ce yanzu sun gamsu da wannan kungiya kuma sun karbeta hannu bibbiyu, don haka za su taimaka wajen ganin majalisar tarayya ta amince da qudurin kafa kungiyar da ke gaban majalisa.
Ya yi kira ga al’ummar Najeriya musamman na arewa, su fito su shiga kungiyar a tafi da su tare, kada su yi sakaci a tafi a bar su a baya.