Abba Ya Gurfanar Da Ganduje A Gaban Kotu

0
224
Rabo Haladu Daga Kaduna
ABBA Kabir Yusuf, mutumin da Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya kayar a zaben Gwamna na shekarar 2019, ya gurfanar da Ganduje a gaban kuliya.
Sai dai wannan karon ba batu ne na zargin yin magudin zabe ba.
Abba Kabir Yusuf ya shigar da kara gaban kotu yana mai kalubalantar matakin da Gwamna Ganduje ya dauka na mallaka wa wasu fitattun ‘yan kasuwa, masu kamfanonin Mudatex da El samad, otal na Daula da kuma tashar zamani ta Shahuci da ke cikin birnin na Kano.
Lauyan tsohon dan takarar Gwamnan, Barista Bashir Yusuf, ya ce hakan ya ci karo da kundin tsarin mulkin Najeriya da yake magana kan hakkin mallakar ƙasa ko fili.
Sai dai bangaren gwamnati ya ce har yanzu ba su da labarin shigar da karar.
Abin da ya faru a kotu
Kazalika lauyan Abba Kabir Yusuf ya ce akwai batun bashi na gina layin dogo mai amfani da lantarki da gwamnatin ta shirya ciyowa daga kasar China wanda ya ce idan aka karbo za a jefa Kano a cikin mawuyacin hali na durkushewar tattalin arziki.
Sai dai lauyan gwamna wanda kuma shi ne Kwamishina Shari’a na jihar Kano, Barista Musa Lawan, ya ce ko kadan babu kanshi gaskiya a cikin labaran da ake yadawa game da bayar da filayen.
Ya ce an bai wa wani kamfani na H & I tashar motar zamani ta Shahuci ne don yin shaguna na zamani da zai sayar da su ga ‘yan kasuwa kamar yadda gwamnatin jihar ta yi a kasuwar Dangauro da ke titin Zaria a Kano.
Ya kara da cewar layin dogon kuma tsohon aiki ne domin kuwa sai da gwamnati ta sami amincewar Gwamnatin tarayya sannan Ita kuma gwamnati China ta bayar sa bashin da ake magana a kai.
Barista Musa Lawan ya ce otal na Daula shi ma kwatankwacin hadin guiwa da gwamnatin Kano ta shiga da sauran kamfanoni ne amma ba ta mallakawa kowa shi ba.
A cewarsa, hasalima tana duba yiwuwar yadda za a bai wa masu sha’awar zuba jari dama, sannan kasuwar zamani zaa samar a wurin kamar dai yadda shi mai kamfanin Mudatex ya nema.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here