Sabon Shugaban Kasuwar Dawanau Ya Kama Aiki.

0
462

Shugaban Kasuwar Dawanau, Alhaji Sani Ahmed Kwa.

Jabiru A Hassan, Daga Kano.
SABON shugaban kwamitin riko na kasuwar Mayan abinci ta duniya dake Dawanau Alhaji Sani Ahmed Kwa ya kama aiki tareda fara tsara yadda harkokin kasuwar zasu ci gaba da tafiya bisa la’akari da yadda kasuwar take kara bunkasa.
Wakilin mu Wanda ya ziyarci kasuwar, ya ruwaito cewa al’amura sun fara tafiya cikin nasara, sannan sabon shugaban yana ci gaba da ganawa da rukuni rukuni na  yan kasuwar  domin shawar ta yadda za’a samar da ci gaba mai kyau a wannan guri wanda yake karbar bakuncin mutane daga kowane sashe na fadin duniya.
Bugu da kari, duk da cewa sabon shugaban Alhaji Sani Ahmed Kwa ya sami kasuwar ta Dawanau da matsaloli masu tarin yawa, ana yi masa kyakykyawan zaton cewa kafin wa’adin da aka bashi na rikon wannan kasuwa zai yi amfani da kwarewarsa wajen kawo sauyi da tsaftace komai ta yadda za’a ci gaba da amsa sunan ta na matsayin kasuwar kayan abinci ta duniya.
A zantawar sa da wakilin mu, Alhaji Sani Ahmed Kwa yace da yardar Ubangiji zai yi kokari wajen kawo ci gaba mai inganci a kasuwar ta Dawanau tareda samar da yanayi na kasuwanci mai albarka musamman ganin yadda matsayin ta yake a idon duniya, sannan yayi alwashin cewa zasu jawo mutane yan kaauwa  domin yin hulda ta kayan abinci daga sassa daban-daban na wannan kasa da Afirka dama sauran kasashe na duniya.
Dangane da kalubalen dake gabansa kuwa, Alhaji Sani Ahmed Kwa yace” zamu hada hannu da sauran yan kwamiti muyi aiki da gaske wajen kawo ci gaba a kasuwar Dawanau, kuma zamu bi duk wani kalubale sannu a hankali domin ganin an magance shi musamman ganin cewa shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa Alhàji Ado Tambai Kwa mutum ne wanda yake sauraron bukatun al’uma batare da tsaiko na”. Inji shi.
A karshe, sabon shugaban kasuwar ta Dawanau yayi godiya ga abokan aikin da watau yàn kwamitin rikon kasuwar da dukkanin yan kasuwar manyansu da kanana saboda kokarin da suke yi wajen tabbatar da cewa kasuwar tana samun ci gaba mai kyau.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here