Ina Garkuwa Da Mutane Ne Domin Tara Kudin Sadaka – Malamin Coci

0
273

Daga Usman Nasidi.

RUNDUNAR ‘yan sandan Nigeria a ranar Laraba ta gurfanar da wani tsohon malamin coci, Adetokunbo Adenokpo, bisa zarginsa da yin garkuwa da wani dan aike.

Bayan yin garkuwa da dan aiki ne, Mista Adenokpo ya boye shi a dakin da ke karkashin cocin, a Sagamu, jihar Lagos.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar DCP Frank Mba, ya gurfanar da Adenokpo tare da wasu mutane 34 da ake zarginsu da laifuka daban daban, a shelkwatar rundunar da ke yaki da fashi da makami a Abuja, a ranar Laraba.

Malamin cocin ya ce ya yanke shawarar shiga harkar garkuwa domin tara kudaden da zai raba wa mabukata sadaka.

Ya ce duba da cewa bukukuwan babbar Sallah na gabatowa, ba shi da kudi, dole ya nemi kudin da zai sai kayayyaki kamar shinkafa, wake, rago da sauran su domin rabawa mabukata.

Malamin cocin ya ce shirin bayar da tallafin bai tsaya akan addinin kirista kawai ba, har da sauran addinai.

DCP Mba ya ce dan aiken Job Ekpe Jonathan, na aiki ne da kamfanin tura sakonni na Glory Master, ya shiga komar Adenokpo da tawagarsa ne a lokacin da ya kai wasu kayayyaki cocin.

Mba ya ce malamin cocin, wanda shi ne shugaban cocin Newlife Church of God da ke Sagamu, ya yiwa dan aiken allurar anesthesia domin galabaitar da shi don basu saukin daure shi.

Rundunar ‘yan sanda ta kaddamar da bincike da kuma samun damar ceto Jonathan a inda aka daureshi, wani daki dake karkashin cocin.

Malamin cocin, wanda aka cafkeshi tare da abokan aikinsa, ya ce yayi shekaru 22 a harkar malinta, bayan da ya samu horo a Ibadan.

“A cocina, muna da shirin bayar da sadaka, inda muke raba kayan abinci da na masarufi ga mabukata, kuma hakan ya bunkasa a lokacin COVID-19.

“Ina jin takaici idan mutane suka zo neman taimako a wajena, alhalin ba ni da kudi a asusun bankina,” a cewarsa.

Ya ce an gina dakin karkashin kasar ne inda ya boye Jonathan lokacin da aka kai masa farmaki kwanakin baya, kuma an yi shi ne domin ya zama mafakarsa idan aka kawo masa hari.

Ya ce yana da wasu matasa da ke bashi kariya.

“Makonnin da suka wuce, na fahimci kudina sun kare. Sai na yi tunanin yin wani abu ga Ileya don samun buhunan shinkafa, wake , man ja da sauran kayan da za a raba wa mabukata.

“Sai na yi shawarar mu yi wa kamfanoni masu arzikin gadar zare, ta hakan za mu rinka tara kudaden da za mu tallafa wa mabukata.

“Mu uku ne muka yi garkuwa da Jonathan da nufin tara kudin da zamu raba wa Ileya. Na yi masa allura ne saboda na ga yana kokarin guduwa, ba na so kuma a ji masa rauni,” a cewarsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here