Kungiyar Boko Haram Ta Sare Kan Wasu Jagororin Kungiyar a Da Ke Tafkin Chadi.

0
354
Muhammad Sani Gazas Chinade, Daga Damaturu

Wani rahoto daga Yankin Tafkin Chadi na nuna cewar sababbin shugabannin kungiyar ‘yan ta’addar ISWAP da majalisar shura sun hallaka wasu manyan jagororin yakin ‘yan ta’addar. Daga cikin wanda aka kashe sun hada da wani babban mayakin kungiyar, Baba Kaka, wanda ya shafe shekaru hudu ya na jagorantar ta’adin da ISWAP ta ke yi a cikin yankin tafkin Chadi.
Bayanin na nuna Cewar, wannan hukunci da kungiyar ta Boko Haram da ta hade da ISWAP ta yi ya Samu sahalewar wassu hanshakan Imamai na kungiyar ne dake yankin na Chadi.To bayan Amir Baba Kaka, babban Alkalin ISWAP ya yankewa shehin Malamin kungiyar, Ba’a Masta, da wasu mutane 14 hukuncin kisa, kuma ana sa ran fille kansu bayan bikin Idi. Rahotanni sun ce sabon shugaban ISWAP, Amir Abubakar Lawan ya nada Amir Goni Maina a matsayin gwamnan shiyyar Tunbu bayan an yankewa Baba Kaka hukuncin kisan kai.
A ranar Lahadi, 26 ga watan Yuli, aka sare kan tsohon shugaban a dajin Kwalaram tare da wasu manyan sojojinsa; Amir Muhammed Lawal wanda aka fi sani da Abba Lawal da Amir Musa. “Bincike da hukuncin kisan da aka yankewa Amir Baba Kaka da yaransa biyu ya dauki tsawon makonni hudu.”
Alkalin alkalan ISWAP, Amir Malumma da ‘yan majalisarsa; Malam Ibrahim, da babban Malamin Boko Haram, Malam Sa’ad da Bako Fulgori su na cikin wadanda su ka yi wannan shari’a. Rahoton ya kara da cewa an kashe Kaka ne domin Amir Abubakar Lawan da babban na-kusa da shi, Abu Musab Al-Barnawi su kara samun karfin iko a tafiyar ‘yan ta’addan.
“Ana fahimtar mafi yawan sojojin da aka kashe ko aka yankewa hukuncin kisa sun taka rawar gani wajen kifar da gwamnatin ‘dan tsohon shugaban Boko Haram, Abu-Musab Al-Barnawi.” Shari’ar da aka yi ya nuna cewa Alkali ya samu Amir Baba-Kaka da aikata manyan laifuffuka. “Wadannan laifuffuka sun hada sabawa umarni, rashin adalci, satar dukiya, cin kudin haraji, tunzura cin amana, da kuma kisan gilla.” “Sauran laifuffukan sun hada da gaza rike iyakarsa a lokacin da ya ke gwamnan Tumbus.” ISWAP ta na zargin cewa rashin kokarin tsohon gwamnan ya sa sojojin MNJTF su ka samu galaba a kan Boko Haram a kwanakin da ya Kai ga kungiyar rasa wasu dakarunsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here