Najeriya Da Amurka Sun Cimma Matsaya Kan Yarjejeniyar Sufurin Jiragen Sama

0
253

Daga Usman Nasidi.

GWAMNATIN Najeriya ta amince da sa hannu kan wata jarjejeniya ta sufurin jiragen sama, tsakanin Najeriya da gwamnatin kasar Amurka.

Ministan watsa labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin da yake jawabi ga manema labarai na fadar shugaban kasa.

Ya yi jawabin ne bayan fitowa daga taron majalisar zartaswa karo na 10 da aka gudanar ta yanar gizo wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.

Mohammed, wanda ya yi magana a madadin ministan sufuri, Sanata Hadi Sirika, ya ce yarjejeniyar zata bunkasa tattalin arziki, ci gaban rayuwa da al’adu na kasashen biyu.

A cewarsa: “Ministan sufuri ya gabatar da wata takarda a ranar Laraba inda ya bukaci a sa hannu kan yarjejeniyar sufurin jiragen sama tsakanin Nigeria da Amurka.

“Ministan ya bukaci amincewar majalisar domin sa hannu kan wannan yarjejeniya wacce take da muhimmanci wajen bunkasa alakar Nijeriya da USA.

“Za ku iya tunawa cewa da Amurka da Nijeriya abokan juna ne a taron Chicago da aka yi a ranar 7 ga watan Disamba, 1994.

“Tambihi na 6 na taron ya kawo bukatar kasashe su sa hannu kan yarjejeniyar sufurin jiragen sama domin bunkasa alaka ta siyasa, tattalin arziki da bunkasa rayuwa.

“Tuni kasar Amurka ta sa hannu a nata bangaren, kuma a yau shugaban kasa da kafatanin majalisar sun amince kuma sun sa hannu kan yarjejeniyar.

“Don haka, shugaban kasa ya rattaba hannu kan yarjejeniyar sufurin jiragen sama tsakanin Nijeriya da Amurka da nufin amfanar kasashen biyu, musamman ma Nijeriya a kokarinta na ganin ta mallakin nata kamfanin jirgin sama.

“Don haka, za mu yi amfani da wannan damar wajen bunkasa tattalin arziki, al’adu da bunkasa rayuwa tsakaninmu da Amurka.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here