‘Yan Bindiga Sun Kashe ‘Ƴan Gida Ɗaya Su 13 A Kogi

0
639

Daga Usman Nasidi.

‘YAN bindiga sun kashe mutum 13 ‘yan gida daya a ranar Laraba a wani hari da suka kai da safe a garin Agudu da ke Bassa a karamar hukumar Kogi/Koton-karfe na jihar Kogi.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kogi, Ede Ayuba ya tabbatar wa manema labarai afkuwar wannan lamarin a ranar Laraba.

Ya kara da cewa sun kuma sake kashe mutum daya yayin da suka raunata mutum shida da a yanzu suke asibiti suna karbar magani.

Kwamishi nan ya ce sun amsa kira nan take bayan an sanar da su amma a lokacin da suka isa wurin yan bindigan sun tsere.

Ya ce a halin yanzu dai an samu zaman lafiya a garin kuma kowa ya cigaba da harkokinsa kamar yadda ya saba.

Ayuba ya ce akwai yiwuwar rikici tsakanin garuruwa da aka dade ana fama da shi a jiha ne ya janyo harin.

Ya bayyana harin a matsayin abin takaici, “domin an kashe Mai gida da iyalansa guda 12, mutum daya kadai ya tsira a gidan.”

Ya kuma ce an kama wadanda suka kashe Innocent Ofodile, mutumin da ya ke da fitattacen Kantin Chucks Supermarket a Lokoja da aka kashe a hanyar Lokoja zuwa Abuja.

Ya ce an kama wani Victor Omogor daga nan kuma ya tona asirin sauran abokansa da ya ce sun aikata mummunan lamarin tare.

A cewar Omogor, daya daga cikin maaikatan mutumin da ke aiki a shagonsa ne ya umurci su kashe marigayin saboda ya ki taimaka masa da kudi a lokacin da mahaifinsa ya rasu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here