Yau Take Babbar Sallah: Buhari Ba Zai Karbi Gaisuwar Sallah Ba

0
332

Rahoton Z A Sada

YAU Juma’a milyoyin musulmai a fadin tarayyar Najeriya suke gudanar da ibadar sallar Idi babba wadda ake kira Eid–Adha, bayan mahajjata na duniya da kasar Saudiyya ta amince masu da su yi aikin hajjin bana sun hau arfa jiya. Wannan rana kuma ta zamar wa Musulmi ranar Idi biyu kenan a hade.

A nan gida Najeriya, rahoton da muke samu daga fadar shugaba kasa, Muhammadu Buhari na nuna cewa, shugaban zai yi sallar Idin ne tare da iyalansa a can gida kamar yadda ya yi a watanni biyu baya na karamar sallah. Mai magana da yawun shugaban kasar ne, Malam Garba Shehu ya sanar da haka.

Ya kara da cewa, shugaba Buhari zai yi sallar Idin ne kamar yadda aka tsara domin kiyaye lafiyar al’umma da kamuwa da cutar Covid 19 wajen samar da tazara da sanya takunkumi. Haka kuma shugaba Muhammadu Buharin ba zai karbi gaisuwar sallah daga ‘yan siyasa da sarakunan gargajiya da masu hannu da shuni da malaman addini da ‘ya’yan jam’iyya da sauransu ba domin kaucewa fadawa rikicin kamuwa da cutar korona bairos.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, shugaba Muhammadu Buhari na yi wa daukacin musulman Najeriya na cikin gida da wadanda ke sauke faralin aikin hajji da na duniya baki barka da sallah da fatar Allahh ya nuna mana ta badi lcikin koshin lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here