Ba Zan Iya Tuna Adadin Mutanen Da Na Kashe Ba – Tsohon Ɗan Boko Haram

0
769

Daga Usman Nasidi.

DAYA daga cikin tubabbun ‘yan Boko Haram Abdulwahab Usman ya ce bai taba tsamanin zai samu irin kulawar da aka yi masa ba daga gwamnatin tarayyar Najeriya.

Usman, wanda dan asalin garin Bama ne daga jihar Borno yana daya daga cikin tubabbun ‘yan Boko Haram da suka kammala shirin sauya tunani da halayya na DRR a watan Yuli.

A shekarar 2016 ne Rundunar Sojojin Najeriya ta kaddamar da shirin na musamman na Operation Safe Corridor domin sauya wa tubbabun ‘yan ta’adda tunani kafin mayar da su cikin al’umma.

Usman ya ce shi ba zai iya tuna adadin mutanen da ya kashe ba saboda yawansu amma duk da hakan gwamnati ta yi masa afuwa bayan ya mika wuya.

“Babu wanda aka kashe a cikinmu yayin shirin na sauya mana tunani. Na ji dadin zama na a sansanin domin mafi yawancinmu ba mu yi tsamanin gwamnatin Najeriya za ta kyautata mana haka ba. Sun kula da mu sosai,” inji shi.

“Sun koyar da mu sana’o’i da dama. An koya mana sana’o’i da dama a cikin sansanin kamar aski, walda, kafinta da sauransu. Amma ni na zabi aski. Idan na koma garinmu zan ci gaba da aski. Ba zan koma Boko Haram ba.

“An ba mu Kur’ani mai girma saboda mun tabbatar za mu zama ‘yan kasa nagari. Ba zan koma Boko Haram ba duk wuya ko azaba saboda gwamnati ta kula da mu.

“An tilasta min shiga kungiyar kimanin shekaru biyar da suka shude. Ba zan iya tuna adadin mutanen da na kashe ba da na ke Boko Haram saboda suna da yawa. Boko Haram sun zo kauyenmu suna neman matasa kuma a lokacin ne aka tilasta wa ni da abokai na shiga kungiyar. Daga baya sun tsere sai sojoji suka kai mu barakinsu da ke Giwa a Borno.”

Tsohon dan ta’addan kuma ya roki gwamnati ta ba wa sauran mayakan kungiyar tabbacin cewa za a yi musu afuwa idan har za su mika wuya.

“Gwamnatin Najeriya ta rubuta takarda a hukumance na tabbatar musu da cewa ba za a kashe su ba idan sun mika wuya,” inji shi.

Ya kara da cewa shi da sauran takwarorinsa 602 sun mika wuya ne bayan sun gani a rubuce cewa za a amshe su a kai su sansanin gyaran hali idan suka tuba.

Mutane da dama dai suna nuna kin amincewarsu da shirin gwamnati na sakin tubabun ‘yan ta’addan su koma cikin mutane.

Mazauna Borno da suka yi magana da The Cable sun ce gwamnatin ta ci gaba da ajiye su a hannunta.

Sanata Ali Ndume mai wakiltan Borno ta Kudu shi ma ba ya goyon bayan shirin sauya wa ‘yan Boko Haram halaye inda ya ce ‘yan ta’adda ba za su taba tuba ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here