Home Kasuwanci Ban Da Yin Karya, Ka Canza Shekarka Kawai Dogara – Kauran Bauci

Ban Da Yin Karya, Ka Canza Shekarka Kawai Dogara – Kauran Bauci

0
280
Gwamnan Al'umma Bala Muhammad

Rahoton Z A Sada

GWAMNAN jihar Bauchi ya mai da martani ga Yakubu Dogara cewa idan ɗan siyasa zai sauya sheƙa “bisa wani hasashen samun muƙami, to bai kamata ya yi ƙarya ba, bai kamata ya kawo husuma ba”.

Sanata Bala Mohammed dai ya bayyana fitar tsohon shugaban majalisar wakilan daga jam’iyyarsu ta PDP zuwa tsohuwar jam’iyyarsa ta APC a matsayin wata asara kuma abin takaici.

Yayin zantawarsa da BBC a karon farko tun bayan sauyin sheƙar Yakubu Dogara, Gwamnan ya ce ana hasashen Dogara ya fita ne don neman wani muƙami don haka “ina yi masa fatan alheri”.

Ranar 24 ga watan Yuli ne, aka sanar da komawar tsohon shugaban majalisar zuwa jam’iyya mai mulki, daga bisani kuma ya dangantaka sauyin sheƙar da rashin shugabanci nagari a jiharsa ta Bauchi.

Sai dai Gwamna Bala Mohammed ya bayyana takaicin cewa bai kamata ɓatanci ya zama hanyar ban kwana kafin barin babbar jam’iyyar adawar ta Najeriya ba.

“Shi yana ganin, shi ya mana alheri muka zama gwamna. Mu kuma muna ganin mu muka taimaka masa shi ma ya zama. Amma shi fa Allah, shi ke ba da mulki,” in ji Ƙauran Bauchi.

Ya ce bai dogara da Dogara kafin zamansa Gwamna ko Sanata a jiharsu ta Bauchi ba. A cewarsa asara ne matasan ‘yan siyasa kamar Dogara su riga biyewa son zuciya “saboda yaudara da ƙarya da kuma ruɗi”.

Shi dai Yakubu Dogara ya ce ba gaskiya ba ne zargin da wasu ke yi cewa ya sauya sheka ne saboda burin neman wata dama a jam’iyyar APC.

@YAKUBDOGARA

Saɓanin haka a cewarsa, ya fita ne saboda matsalolin da suka haɗar da ba da kwangiloli ba bisa ka’ida da Gwamna Bala Mohammed yake yi da kuma rashin biyan ma’aikata albashi a kan lokaci.

Ya kuma koka a kan rashin gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomi cikin wata shida na farko, kamar yadda Bala Mohammed ya yi alkawari.

Ya kuma yi zargin cewa: ”Gwamnati ta ciyo bashi na naira biliyan hudu, daga baya aka gano kudin a asusun wani kamfani, duk da yake an ranto su ne da sunan jihar Bauchi, baya ga ninka kudin kwangiloli da ake yi”.

Sai dai gwamnan ya musanta rashin bin ƙa’ida wajen bayar da kwangiloli. Ya ce gwamnatinsa ce ma ta kawo dokar ba da kwangiloli da kuma rage kuɗaɗen aiwatar da ayyukan raya ƙasa.

@YAKUBDOGARA

Ya ce: “Na zo na samu, aikin da za a yi shi a biliyan bakwai, ana yin sa a biliyan goma. Misali hanyar nan da ta taso daga Awala zuwa Meri”.

A cewarsa gwamnatiin da suka gada ta ba da kwangilar ce a kan sama da naira biliyan goma, amma gwamnatinsa ta cimma yarjejeniya da ‘yan kwangilar waɗanda ya ce su da kansu sun yarda an tsuga kuɗi.

Bala Mohammed ya ce duk kwangilolin da suka bayar, sukan ba da su ne bisa ƙayyadajjen tsarin da ake amfani da shi ne a ko’ina cikin faɗin duniya.

Ya ce fitar Yakubu Dogara daga PDP ba ta rasa nasaba da batun masu iya magana da ke cewa “In ka ga kare yana gudu, ko ana bin sa ne, ko kuma shi yana bin wani abu ne ya kama”.

A matsayinsa na babban ɗan siyasa wanda ya riƙe muƙamin shugaban majalisar wakilai kuma mutum na huɗu a Najeriya. Yana ma iya zama ko shugaban ƙasa ko wani abu daban ma, cewar Bala Mohammed.

Sai dai ya ce duk da yake rabuwa da Dogara asara ce gare su amma hakan ba zai zame musu giɓi ba ko illa ba, don kuwa a cewarsa suna tare da al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

%d bloggers like this: