Dan Majalisa Alhaji Lawan Shehu
Jabiru A Hassan, Daga Kano.
DAN Majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Bichi Alhaji Lawan Shehu ya mika sakonsa na barka da Sallah ga daukacin al’umar mazabarsa, tare da fatan ci gaba da samun zamantakewa mai albarka a fadin duniya baki daya.
Ya mika wannan sako ne ta hannun mataimakinsa na musamman, Alhaji Garba Sadah Bichi cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun wannan hadimi nasa, tare da yin addu’ar kawo karshen annobar cutar Corona Virus wadda ta zamo barazana a duniya.
Alhaji Lawan Shehu ya kuma yi fatan alheri ga gwamnan jihar kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje da mataimakainsa Dokta Nasiru Gawuna da shugaban majalisar dokokin jihar Kano Alhaji AbdulAzeez Garba Gafasa da dukkanin ‘yan majalisar dokokin jihar ta Kano bisa kammala Babbar Sallah lafiya.
Haka kuma Dan Majalisa Lawan Shehu ya yi amfani da wannan dama wajen isar da sakon barka da Sallah ga mai martaba Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero da dukkanin hakimansa da sauran masu rike da sarautar gargajiya da malamai da kuma shugabannin Jam’iyyar APC na karamar hukumar ta Bichi.
A karshe, dan majalisar ya yi fatan cewa kyakykyawar dangantaka da ke tsakaninsa da al’umar karamar hukumar ta Bichi za ta ci gaba da tafiya cikin nasara ta yadda za a sami managarcin ci gaba mai amfani a mazabar.