Duk Zarge-zargen Da Ake Yi Mini Karya Ne – Mamman Daura

0
337
Marigayi Sama'ila Isa Funtuwa da Abba Kyari duk aminan Mamman Daura ne...
Mustapha Imrana Abdullahi
DAYA daga cikin makusantan shugaban tarayyar Nijeriya Malam Mamman Daura ya bayyana cewa duk maganganun da wadansu mutane ke yi masa ba gaskiya ba ne.
Mamman Daura ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da kafar yada labarai ta bbc hausa.
Mamman Daura ya kuma ce tun a lokacin marigayi Sardaunan Arewa ya zabe su suka je karatu kasar Ingila, kuma game da batun cin hanci kuwa Malam Mamman Daura ya ce daman can akwai shi kodayaushe tun tale-tale.
“Ai ba ka yi wa gwamnati katsalandan, ko shawara ce sai an tambaye ni, amma ba haka kawai ba, kuma shekaru sama da Arba’in muna tare da marigayi Abba Kyari tun da muka yi aiki tare da shi a kamfanin jarida na New Nigeria, kuma shi yana cikin gwamnati ni kuma ina daga waje ne ba kamar yadda ake yin zargi ba”.
Mamman Daura ya kuma tabbatar da cewa kokarin marigayi Malam Abba Kyari ne ya sa aka samu kamfanonin hada Taki 31 kusan dukkan wannan tashin kamfanoni kokarinsa ne.
Shi kuma Marigayi Alhaji Sama’ila Isa Funtuwa suna tare da shi shekaru 40 kenan kuma sun hadu ne tun a lokacin suna aiki a masakar UNTL da ke garin Kaduna, lokacin marigayin yana matsayin shugaban kula da ma’aikata na kamfanin UNTL, ni kuma ina Darakta tun daga nan muka shaku kwarai, har muka je muka kafa masakar Funtuwa duk muna tare har rasuwarsa, don haka rasuwar mutanen nan biyu ya kidima ni kwarai domin na ji a jikina sosai.
Mamman Daura ya ci gaba da bayanin cewa shugaba Buhari Kawunsa ne domin kanin mahaifinsa ne, to, ta yaya za a rika yada irin maganganun da ake yi?
Kuma a lokacin da ake yi wa wani hukuncin cin hanci ko da kashe wanda ya yi shi aka yi a lokacin ne za ka ga wani kuma ya kara aikata laifin don haka daman can akwai batun cin hanci da karbar rashawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here