Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Tsokacinta Na Farko Kan Jawabin Mamman Daura

0
250

Daga Usman Nasidi.

FADAR shugaban kasa ta yi tsokaci kan kan kiran da aminin shugaba Muhammadu Buhari, Mamman Daura, ya yi cewa a daina amfani tsarin zagaye a kujeran shugaban kasa inda Mamman Daura ya ce kawai a bi cancanta.

Daura ya bayyana hakan ne a hirar da ya yi ga BBC Hausa a makon da ya gabata inda kungiyoyi daban-daban sukayi masa martani.

Shekaru 20 yanzu kenan ana amfani da tsarin zagaye a kujeran shugaban kasa tsakanin kudu da Arewa.

A tsokacin farko, fadar shugaban kasa a ranar Laraba ta ce jawabin Malam Mamman Daura ra’ayinsa ne kawai ba na gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ba.

Mai magana da yawun Buhari, Malam Garba Shehu, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki a shafinsa na sada zumunta inda ya ce: “Yana da muhimmanci mun bayyana kamar yadda wanda aka yi hira da shi ya ambata inda ya ce maganganun da ya yi ra’ayiyinsa ne, amma, ba na shugaban kasa ko gwamnatinsa.”

Garba Shehu ya ce mutane sun yi wa jawabin mumunan fassara.

Wannan ya biyo bayan tsokacin kungiyoyi irinsu Middle Belt Forum, Ohanaeze Ndigbo, Afenifere da South-South Elders’ Forum ta mutanen Arewa , Ibo, Yarbawa, Neja-Delta kan maganar Mamman Daura.

A hira da kungiyoyin su ka yi da jaridar a mabanbantan lokaci, sun nuna ba su goyon bayan kiran da Mamman Daura yake yi. Sai dai kungiyar ACF ta manyan Arewa ta ce dattijon ya yi gaskiya.

Shugaban kungiyar Ohanaeze Ndigbo, Cif Nnia Nwodo, ya yi magana ta bakin hadiminsa, Emeka Attamah, ya na mai cewa akwai son rai a kalaman da ‘dan uwan shugaban kasar ya yi.

Nnia Nwodo ya tuna wa Mamman Daura cewa an fatattaki Goodluck Jonathan daga mulki a 2015 ne saboda mutanen yankin Arewa suna ganin cewa lokacinsu ne da za su yi mulkin kasar.

Hakazalika kungiyar matasan Ohanaeze ta bayyana cewa adalci da nuna daidaiton da shugaba Muhammadu Buhari zai iya yi kadai shi ne ya mika ragamar mulki hannun dan kabilar Igbo a 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here