Kowane Mutum 1 Cikin Mutane 10 A Jihar Kaduna Na Shan Kwaya

0
231

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

DARAKTA Janar na cibiyar hana ta’amuli da kwayoyi a jihar Kaduna, Dakta Joseph Maigari, ya ce kashi 10.9% na mazauna jihar Kaduna na ta’amuli da muggan kwayoyi.

Joseph Maigari ya bayyana hakan ne yayinda yake hira da manema labarai kan abubuwan da cibiyar kaeyi.

Ya ce safiyon da aka gudanar wannan shekaran a fadin jihar ya nuna cewa a cikin kananan hukumomin jihar 23, an samu mutum 11 cikin kowani 100 na ta’amuni da muggan kwayoyi.

Ya ce amma hukumar tana aiki da wasu kungiyoyi masu zaman kansu da ma’aikatun gwamnati wajen rage shan kwaya a jihar.

A cewarsa, “Wani safiyon da aka gudanar ya nuna cewa kashi 10.9% na mazauna jihar Kaduna na da matsalan ta’amuni da kwayoyi.”

“Jiharmu kadai ce ta gudanar da safiyon sanin ainihin matsalan ta’amuni da kwaya a Najeriya.”

“Yaki da ta’amuni da kwayoyi a Najeriya ya kasance damke masu safarar kwayoyin, amma kamar yadda muka gani, (hakan bai haifar da ‘da mai ido ba), ba zamu iya samu nasarar yakar kwaya da bindiga ba.”

“Wajibi ne mu janyo hankalin mutanenmu wajen daina amfani da kwayoyi. Shi yasa jihar Kaduna ta kasance jihar farko a Najeriya mai dokan hana kwaya mafi kyau a Najeriya.”

Ya ce jihar na gina gidajen gyara yan kwaya a Ikara, Chikun, Igabi da Kachia.

Ya kara da cewa wannan sabon shiri da gwamnatin jihar keyi ya samu sa hannu da amincewa cibiyar cigaban dan Adam kuma ana shirin magance matsalar kwaya cikin al’ummar jihar Kaduna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here