‘Yan Bindiga Sun Kashe Wani Ɗan Kasuwa A Kaduna

0
636

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

MUTANEN garin Udawa a karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna sun shiga ruɗani yayin da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kashe wani ɗan kasuwa a gonarsa.

An bayyana cewa sunan marigayin ɗan kasuwan Malam Jafaru Bello.

Majiyarmu ta samu rahoton cewa ‘yan bindigan sun kai masa hari ne a lokacin da ya tafi gonarsa a wani gari mai suna Goluwa a safiyar ranar Laraba.

An kuma gano cewa ‘yan bindigan sun yi awon gaba da wasu manoma uku daga gonarsa a ranar da suka kashe shi.

Garin Udawa yana da iyaka da ƙaramar hukumar Birnin Gwari na jihar Kaduna.

Wani jagoran al’umma a garin, Malam Muhammadu Umaru wanda ya tabbatar wa majiyarmu afkuwar lamarin ya ce wanda abin ya faru da shi makwabcinsa ne.

Malam Umaru ya ce, “Irin wannan abin bai taɓa faruwa ba; ta baya aka kashe shi. Makwogoronsa ne kawai ya rage da sun datse kansa. Jafaru makwabcina ne kuma ɗan kasuwa ne mai mata hudu da ‘ya’ya 12.

‘Yan bindiga sun masa kisar rashin tausayi a gonarsa a safiyar ranar Laraba. Sun kuma sace wasu manoma uku sun tafi da su.”

Ya ce ƴan bindigan su kan harbi waɗanda suka kama ne amma yanzu yankan rago suke musu wadda hakan ya jefa ƴan kauyen cikin damuwa.

Mai magana da yawun ƴan sandan jihar bai amsa wayarsa ba.

Amma kwamishinan ƴan sandan jihar, CP, Umar Musa Muri ya ce ba zai iya tabbatar da afkuwar lamarin ba a lokacin da aka tuntube shi.

Ƙaramar hukumar Chikun tana ɗaya daga cikin garuruwan da ake fama da matsalar ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here