Home Kasuwanci An Kashe Fiye Da Naira Miliyan 500 Don Ciyar Da ‘Yan Makaranta...

An Kashe Fiye Da Naira Miliyan 500 Don Ciyar Da ‘Yan Makaranta Lokacin Kulle

0
274

Rahoton Z A Sada

GWANATIN tarayyar Najeriya ta ce ta kashe kimanin naira miliyan 523 da dubu 300 kan shirin ciyarwa a makarantu lokacin kullen cutar korona a ƙasar.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, (NAN) ne ya ambato ministar ayyukan jin ƙai, magance annoba da bunƙasa rayuwar jama’a, Sdiya Farouƙ na bayyana haka ranar Litinin a Abuja.

Ya ruwaito ministar yayin taron gabatar jawabai na kwamitin shugaban ƙasa kan cutar korona na fayyace bayani, sakamakon jita-jita da raɗe-raɗin da ake yaɗawa kan shirin ciyarwa.

@SADIYA_FAROUQTWITTER

Ta ce a Abuja, gida 29,609 ne suka amfana sai Legas gida 37,589 yayin da gida 60,391 suka ci gajiyar shirin a jihar Ogun daga ranar 14 ga watan Mayu zuwa ranar 6 ga watan Yuli.

Ta ce don bin umarnin shugaban ƙasa, ma’aikatarta ta tuntuɓi gwamnatocin jihohi guda uku inda suka amince da yin amfani da tsarin ‘zubin abincin kai wa gida” a matsayin zaɓin ciyar da yara lokacin kulle.

Masu ruwa da tsaki sun amince kuma a fara aiwatar da shirin a babban birnin Abuja da Legas da kuma jihar Ogun, a matsayin zakaran gwaji, in ji ministar.

Sadiya Faruƙ ta ce an kimanta kowanne zubin kwanon abinci a kan naira 4,200 bayan gudanar da cikakkiyar tuntuɓa.

Ta ce an tsai da shawara kan yawan kuɗin ne daga ƙiyasin da hukumar ƙididdiga ta ƙasa da kuma babban bankin Najeriya suka samar.

A cewarta alƙaluman hukumomin sun nuna akasarin magidanta a Najeriya na da iyalin da ya ƙunshi mutum biyar zuwa shida, kuma uku zuwa huɗu a cikinsu sun dogara da shi ne don samun abin rayuwa.

Ministar ta ce don haka suna ƙaddara cewa kowanne gida yana da ‘ya’ya guda uku, kuma a ƙarƙashin shirin ciyarwa a makarantar tun farko, an tsara ne duk yaro yana cin abinci sau ɗaya a kan naira saba’in.

@SADIYA_FAROUQTWITTER

Don haka duk yaro ɗaya na cin abincin naira 1,400 ne a wata ɗaya tsawon kwana 20 da ake zuwa makaranta, kuma idan aka lissafa hakan sau uku ya kama naira 4,200 ke nan, in ji ta.

Sadiya Faruƙ ta ce don tabbatar da ganin an yi komai cikin gaskiya da amana, sun haɗa gwiwa da Shirin Samar da Abinci na Duniya a matsayin ƙwararrun abokan aiki.

Baya ga hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa irinsu EFCC da ICPC da hukumar tsaro ta DSS gami da wasu ƙungiyoyi don bin diddigin tsarin da ake gudanar da shirin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

%d bloggers like this: