‘Ba ‘Yan Boko Haram Ne Suka Kai Min Hari Ba’ – Gwamna Zulum Ya Fasa Kwai

0
410
Daga Usman Nasidi.
GWAMNAN jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya dora alhakin harin da aka kai wa tawagarsa ranar Laraba ta makon jiya a kan sojojin Najeriya.
A ranar Larabar makon jiya ne aka kai wa tawagar gwamna Zulum hari yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa garin Baga da ke karkashin karamar hukumar Kukawa a jihar Borno.
Jaridar Premium Times ta rawaito cewa Zulum ya tsallake rijiya da baya yayin da aka kai wa tawagarsa hari yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Baga domin rabon tallafi ga mazauna sansanin gudun hijira (IDP).
Da yake magana da kwamandan rundunar soji jim kadan bayan kai wa tawagarsa harin, Gwamna Zulum ya nuna bacin ransa a kan yadda sojoji suka gaza kwace garin Baga duk fa yawan rundunoninsu da ke jibge a yankin.
“Kun fi shekara guda a nan wurin, akwai sojoji 1,181 a wannan yankin, idan ba za ku iya kwace garin Baga mai nisan kilomita 5 daga sansaninku ba, sai mu hakura mu manta da Baga.
“Zan sanar da bbban hafsan rundunar soji idan ya so sai ya sauya wa sojojin da ke nan wurin da za a amfane su,” kamar yadda gidan Talabijin na Channels ya rawaito Zulum na fada wa kwamandan sojojin.
Da yake magana kwana daya bayan kai masa harin, Zulum ya ce abin da ya faru a kansa ba wani abu ba ne face kitimurmurar sojoji.
Gwamna Zulum ya bayyana hakan ne yayin da wasu Gwamnonin jam’iyyar APC a karkashin jagorancin shugabansu, Atiku Bagudu Gwamnan jihar Kebbi, suka kai masa ziyarar jaje a fadar gwamnatin jihar Borno da ke Maiduguri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here