Akalla Mutane 78 Sun Mutu A Harin Bam

0
533
Mustapha Imrana Abdullahi

RAHOTANNIN da ke fitowa daga kasar Lebanon na cewa akalla mutane 78 sun rasa ransu a wani harin Bam da aka kai a kasar.
Rahotannin suna cewa a halin da ake ciki mutane na ta neman ‘yan uwansu sakamakon tashin Bam din da aka samu.
Firayim ministan Lebanon Hassan ya shaida wa manema labarai cewa wadanda suka aikata wannan aikin za su yaba wa aya zakinta domin sa a yi masu hukunci dai dai da abin da suka aikata.
Shugaban Kasar Amurka Donald Trump a wani jawabin da ya yi wa duniya ya jajanta wa daukacin mutanen kasar, tare da yin alkawarin taimakawa sakamakon Bam din da ya tashi da a cewarsa ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama tare da raunata wadansu mutane masu yawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here