Home Kasuwanci Za A Rataye Masu Yi Wa Kananan Yara Fyaɗe A Bauchi

Za A Rataye Masu Yi Wa Kananan Yara Fyaɗe A Bauchi

0
829
Gwamnan Al'umma Bala Muhammad

Rahoton Z A Sada

GWAMNATIN jihar Bauchi karkashin jagorancin Gwamna Bala Muhammad ta kafa wata doka da ake kira BAP wadda ta tanadi hukuncin kisa ta hanyar rataya ga duk wanda aka samu da laifin yi wa yara kanana Fyade.

Haka ma dokar ta tanadi ɗaurin rai da rai ga wanda ya yi wa babbar mace fyade da kuma ɗaurin shekaru 20 ga wadanda suka yi wa mace daya taron dangi.

Wannan dai na zuwa ne yayin da hukumomin ‘yan sanda a jihar suka ce sun samu rahotannin aikata fyade har 21 a cikin wata ɗayan da ya wuce kawai.

Ko a baya-bayan nan ma ‘yan sanda a jihar sun sanar da kama wani mutum da suke zargi da yi wa wata yarinya ‘yar shekaru uku fyade.

DSP Muhammad Ahmad Wakili, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ta Bauchi ya ce dokar tuni aka amince da ita a majalisa kuma za a wallafa ta.

A cewarsa, tsakanin watan Yuli da Agusta sun gabatar da mutum 22 da ake zargi da aikata fyade gaban ‘yan jarida.

Ya ce sun yi hakan saboda “muna son mutane su kyamaci wannan abin su gane cewa idan an yi wa mace fyaɗe mai da al’uma baya ne saboda har ta gama rayuwarta da wannan (ƙyamar da ake nuna mata).”

DSP Wakili ya ce laifin fyaɗe ba wai yarinyar da aka yi wa ya shafa ba, laifin ya shafi ƙasa ne.

“Duk wanda muka kama ya yi fyaɗe, ba za mu yi wata-wata ba, sai mun gurfanar da shi gaban kotu, kuma wannan (dokar) BAP ita za mu saka ma shi a gaban kotu.” in ji DSP Wakili.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

%d bloggers like this: