Home Uncategorized ‘Da Sana’ar Jari Bola Na Kammala Karatun NCE’

‘Da Sana’ar Jari Bola Na Kammala Karatun NCE’

0
344

Rahoton Z A Sada

WANI matashi, Isa Muhammad ɗan asalin jihar Katsina da ke gudanar da sana’ar bola jari a Abuja, babban birnin Najeriya ya ce da sana’arsa ta bola jari ya samu har ya shiga makaranta har ya kammala matakin shaidar koyarwa ta NCE.

Isa Muhammad ya shaida wa BBC irin ƙalubalen da ya fuskanta har ya rungumi wannan sana’a. Ya ce da aikin sharar da yake yi a Abuja ne ya riƙa faɗi tashin biyan kuɗin makaranta da wurin kwana.

“Na rasa iyayena ina da shekara 13 sannan rayuwa a wannan lokacin tana da wahala, kamar ni da na fito daga gidan marasa hali,”

“Ka samu kuɗi wanda za ka shiga makaranta abu ne mai wahala, wannan ya tursasani na bar makarantar sakandare, na zo Abuja na samu kuɗi da wannan kuɗi dana samu ina tarawa da shi ne Allah ya sa na ci gaba da makaranta har na gama.” in ji matashin.

A cewarsa, bayan gama sakandare ne ya koma Abuja ya ci gaba da aiki, yana samun kuɗi “na yi JAMB na samu makin da ake buƙata zuwa shiga makaranta ta gaba da sakandare – NCE.”

Ya ce duk da kallon ƙasƙanci da ake yi wa wannan sana’a ta sa, hakan bai sa ya daina ba saboda “ina tashi ƙarfe shida (na safe) bayan na yi sallar asuba, wannan lokacin ne nake tafiya aiki.”

Isa Muhammad ya ƙara da cewa a rana yana samun naira 1,500 zuwa 2,000 ko abin da ya fi haka.

Isa Muhammad dai ya ce yana fatan nan da shekara biyar ya kammala karatunsa na digiri sannan yana da burin taimaka wa mutanen da suma basu da hali domin rayuwarsu ta yi kyau.

Ya kuma shawarci waɗanda suka rasa iyayensu tun suna ƙanana inda ya ce kada su guji yin karatu, “duk yanayin da ka ɗauki kanka, za ka iya taimakon kanka in dai ka wuce shekara 10.” Ya bayyana cewa yana sha’awar zama malamin jami’a a nan gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

%d bloggers like this: