Ipman Ta Umurci Gidajen Mai Su Fara Sayar Da Mai A Farashin N150

0
205
Daga Usman Nasidi.
KUNGIYAR yan kasuwar man fetur masu zaman kansu IMAN, shiyar jihar Kano, ta umurci mambobinta su fara sayar da man fetur a farashin N150 ga lita.
Shugaban kungiyar na jihar Kano, Bashir Dan-Mallam, ya ce umurnin ya biyo bayan sabon farashin sauyin farashin mai da kamfanin PPMC, mai hakkin sanya farashin mai.
A cewarsa, wannan mataki da za su ya bi ya yi daidai da jawabin gwamnati cewa za ta rika canza farashin mai wata-wata dangane da yadda farashin ya canza a kasuwar duniya.
Dan Mallam ya hakaito jawabin PPMC inda ta ce an kara farashin kayan mai zuwa N138.62 ga lita a depot.
Ya ce tuni Depot sun fara sayar musu a farashin N139.5.
Saboda haka, ya umurci dukkan mambobin kungiyar IPMAN dake karkashinsa su fara sayar da litar mai kuma a tabbatar da cewa “kada wanda ya sayar da mai fiye da N150 ga lita.”
Rahotanni sun bayyana cewa a ranar Talata, 4 ga watan Agusta, 2020, hukumar PPPRA mai alhakin tsaida farashin kayan mai a Najeriya ta yi karin Naira shida a kan litar man fetur.
PPPRA ta maida kudin litar man fetur N138.62 a manyan tashoshin kasar. Wannan shi ne kudin da za a saida mai kafin ayi jigilarsa zuwa gidaje a watan Agusta.
Dama can kun ji ‘yan kasuwan kasar su na kokarin ganin an maida kudin litar fetur tsakanin N149 zuwa N150 a dalilin wannan canji farashi da aka samu a tashoshi.
A farkon makon nan ne wani ‘dan kasuwa ya shaida cewa kudin fetur zai iya komawa N150 a gidajen mai a wannan watan da aka shiga.
Mataimakin shugaban kungiyar IPMAN ta manyan masu saida mai a kasa, Abubakar Maigandi, ya ce har yanzu PPPRA ba ta sanar da su sabon farashin da aka sa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here