
Isah Ahmed Daga Jos
FITACCEN malamin addinin musuluncin nan da ke zaune a garin Jos, kuma Daraktan ilmi na Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta kasa [JIBWIS] reshen Jihar Filato, Sheikh Abubakar Bala Imam Gana, ya yi kira ga masu hali da sauran kungiyoyi su rika tallafa wa gidajen kula da kangararrun yara da yaran su kan su, don ganin an gyara tarbiyarsu. Sheikh Abubakar Gana ya yi wannan kiran ne, a lokacin da ya ziyarci gidan kula da Kangararrun yara na garin Jos, tare da cin abinci da yaran.
Ya ce ya zo wannan gida ne don ya ziyarci waxannan yara, ya nuna masu kauna ya yi masu addu’ar Allah ya fitar da su, kuma ya ci abinci tare da su, musamman a wannan lokaci, na babbar sallah domin wadannan yara ‘yayanmu.
Ya ce lallai gwamnatin Filato tana kokari kan yadda take kula da wadannan yara. Domin ana ba su abinci da koya masu sana’o’i. Wannan zai taimaka wa yaran, idan sun fita su sami sana’a.
Ya yi kira ga gwamnatin ta kara jajarcewa wajen tallafa wa gidan, tare da yaran ta yadda za su dada samun karfin gwiwar, gyara halayensu.
Ya yi kira ga masu hanu da shuni su rika tallafa wa irin wadannan yara, tare da irin wadannan wurare saboda mahimmancin da ke tattare, da yin haka.
Ya ce babu shakka idan ana yin haka, kasa za ta zauna lafiya, a rage irin wadannan Kangararrun yara.
Ya yi kira ga yaran kan idan sun fita, su zamanto mutanen kirki masu biyayya ga iyayensu da gwamnati da sauran al’umma baki daya.
Tun da farko a nasa jawabin wani babban jami’i a gidan kangararrun na Jos, Mista Thomas Pam ya bayyana cewa an kafa gidan ne a shekarar 1981, da manufar kada a rika hada manyan mutane masu laifi da kananan yara a gida kurkuku.
Ya ce a gidan akwai yaran da ake kawowa daga kotuna da yaran da suka gagari iyayensu a gida, domin su sanya su a hanya, tagari.
Ya ce ana ciyar da yaran, ana koyar da su sana’o’in kafinta da gyaran takalma da dinki da karatun boko.
Ya mika godiyarsu kan wannan ziyara da aka kawo masu. Ya ce babu shakka wannan ziyara da aka kawo masu, an nuna masu kauna mai tarin yawa.
Ya roki a samar masu da motar hawa, da na’urar kwanfuta da kayayyakin koyar da sana’o’in da za su taimaka wa yaran da aka kawo masu su koyi sana’a.