Home Noma Ƙarin ‘Yan Kungiyar Boko Haram 109 Sun Miƙa Wuya A Kamaru

Ƙarin ‘Yan Kungiyar Boko Haram 109 Sun Miƙa Wuya A Kamaru

0
790

Rahoton Z A Sada

RUNDUNAR haɗin gwiwa ta ƙasashen Afirka ta Yamma ta bayyana cewa suna samun nasara yayin da dakarunta ke ci gaba da yaƙi da ta’addanci a yankin Tafkin Chadi.

An dai samu ƙarin ‘yan Boko Haram 109 da suka ajiye makamansu tare da miƙa wuya ga hukumomi a Kamaru.

Tuni kuma aka miƙa su cibiyar kula da waɗanda suka kwance ɗamarar yaƙi domin basu matsuguni da nema musu sana’ar yi.

Manjo Janar na sojojin Najeriya Ibrahim Manu Yusuf shi ne kwamandan rundunar dakaraun haɗin gwiwa na yankin Tafkin Chadi ya yabawa dakarun game da ƙoƙarin da suke yi na aikin haɗin gwiwa domin shawo kan matsalar tsaro a yankin.

Shi ma kwamandan shiyya ta farko na rundunar haɗin gwiwa da ke birnin Mora a Kamaru, Birgediya Bouba Dobekreo ya ƙara miƙa goron gayyata ga sauran ‘yan ƙungiyar ta Boko Haram da su miƙa wuya.

Ya ce a shirye suke ku karɓi mayaƙan hannu bi-biyu.

Shugaban cibiyar kula da waɗanda suka ajiye makamai a yankin Meri Umar Bishayir ya bayyana cewa sana’ar akasarin tubabbun ‘yan ƙungiyar ta Boko Haram ita ce noma da kiwo.

“Akwai kuma wasu da suka ƙware a wasu sana’oi daban kamar na kafinta da gini da kasuwanci.” inji Shugaban cibiyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

%d bloggers like this: