Covid-19: Buhari Ya Amince Da Tsawaita Dokar Kulle Da Mako uɗu

0
304

Rahoton Z A Sada

SHUGABAN kasa, Muhammadu Buhari ya sake tsawaita dokar kullen da aka sassauta kashi na biyu da makonni huɗu.

Sakataren gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin da shugaban ƙasa ya kafa na yaƙi da cutar korona Boss Mustapha ne ya bayyana hakan a Abuja yayin wani bayani ga ‘yan jarida kan cutar.

Wannan ne dai karo na uku da ake tsawaita kashi na biyu na sassaucin dokar kullen a faɗin ƙasar.

Akwai shawarwari da sakataren gwamnatin ya bai wa shugaban ƙasar kan ci gaba da sassaucin wannan doka, sai dai ba a fito da bayanai kan shawarwarin ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here