Home Kasuwanci Matasa Sun Yi Zanga-zanga A Katsina Kan Tabarbarewar Tsaro

Matasa Sun Yi Zanga-zanga A Katsina Kan Tabarbarewar Tsaro

0
330

Rahoton Z A Sada

MATASA a wasu kauyukan karamar hukumar Dutsin-ma da ke jihar Katsina a arewacin Najeriya sun gudanar da zanga-zanga don nuna fushinsu kan tabarbarewar tsaro a yankin.

Masu mazauna yankin sun shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne a kauyukan Dan-Marke da Sanawa da kuma Turare inda matasa suka rufe babbar hanyar Kankara zuwa Katsina.

Danmusa

Wani dan kato-da-gora da ke aiki a yankin ya shaida wa BBC cewa kwanaki biyu da suka wuce ‘yan bidinga sun kai farmaki a kauyukan Kurecinge, Kurecin Malam dan Marke da kuma Turare inda suka sace abin hannun mutane sannan suka tafi da wasu.

A cewarsa, hakan ne ya fusata matasa suka fantsama kan tituna.

Rahotanni sun ce daga bisani an kai ‘yan sanda sun tarwatsa matasan.

Ba wannan ne karon farko da matasa ke zanga-zanga a jiar ta Katsina ba sakamakon tabarbarewar tsaron jihar.

..

A farkon watan Yuni mazauna kauyen ‘Yantumaki sun gudanar da zanga-zanga kan tabarbarewar tsaron da yankin ke fama da shi.

Bayanai sun nuna cewa matasan yankin sun harzuka ne bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari a kauyen inda suka sace wani malamin asibiti da diyarsa.

Mazauna jihar na dora alhakin wadannan hare-hare kan gazawar hukumomi.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bai wa hukumomin tsaron kasar umarnin kaddamar kakkabe ‘yan bindiga da suka addabi jama’a a jihar ta Katsina sai dai har yanzu ana ci gaba da fuskantar matsalar hare-haren ‘yan bindigar.

A watan jiya, uban kasar Batsari da ke jihar ta Katsina ya shaida wa BBC cewa akwai kimanin mata 600 da aka bari da marayu sakamakon hare-haren ‘yan bindiga da suka kashe mazajensu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

%d bloggers like this: