Tsofaffin Daliban KTC, Sun Samar Da Sabbin Bencin Karatu 531

0
245

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

KUNGIYAR tsofaffin dalilan Kwalejin  Malamai ta Jihar Katsina, wato Katsina Teachers College (KTC), ta kammala shirin gabatar da sabbin bencin karatu guda dari biyar da talatin da daya ga gwamna Aminu Bello Masari a matsayin gudummawar su ga kwalejin.

Sakataren yan ajin shekarar 1979, Alhaji Kabir Lawal Ruma ne ya bayyana hakan a garin Kaduna yayin da yake yi wa manema labarai karin haske game da shirye-shiryen taron da ke tafe a ranar Talata.

Alhaji Kabir Lawal ya bayyana cewa sabbin ababen zaman dari biyar da talatin da daya zasu samar da wurin zama na akalla dalibai dubu daya da dari biyar da tamanin da daya a kwalejin.

Ya kuma kara da cewa daliban da suka kammala karatun shekarar 1979 sun gyara kujeru dari uku da talatin da hudu wanda za su ba wasu daliban fiye da dalibai dubu daya samun wurin zama.

Sakataren ya ce kafin wannan ci gaban, yan ajin shekarar 1979 sun gina ajin karatu guda biyu da samar da kayan karatu a dakin ajiyar litattafai ga kwalejin.

Ya yaba wa gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina saboda kashe sama da naira miliyan dari uku kan aikin gina sabbin ajuzuwan karatu sama da guda arba’in, kana da yin wasu gyare-gyare da Samar da kayan koyarwa ga makarantar.

Ya shawarci tsoffin dalibai da su yabawa kokarin gwamnati wajen samar da kyakkyawan wuraren koyar da karatu a kasar.

Ya kara da cewa gwamnati ita kadai ba za ta iya samar da dukkan abubuwan da ake bukata na koyarwa da ilmantarwa ba tare da taimakon masu ruwa da tsaki ba.

An gina Kwalejin Malamai na Katsina a cikin 1921 kuma ta kasance tsohuwar cibiyar samar da ilimi a arewacin Najeriya.

Cibiyar ta samar da manyan ‘yan Najeriya da suka hada da Firimiyan Najeriya, Alhaji Sir Abubakar Tafawa Balewa, Firimiya na farko a Arewacin Najeriya Sir, Ahmadu Bello Sardauna na Sakkwato da Sir, Kashim Ibrahim gwamnan farko na Arewacin Najeriya da Dakta Shehu Idris Sarkin Zazzau.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here