An Sake Kashe Mutane 33 A Kudancin Kaduna

0
259
Usman Nasidi, Daga Kaduna.
AKALLA Mutane talatin da uku suka rasa rayukansu wanda yawancinsu yara ne a yayin da ‘yan bindiga dadi suka sake kai hari kauyukan masarautar Atyap da ke karamar hukumar Zangon Kataf ta jihar Kaduna amma hukumar ‘yan sanda ta ce mutane 21 aka kashe.
Rahotanni sun bayyana cewa hare-haren sun auku ne lokaci guda tsakanin karfe 11 na daren Laraba da karfe 1 na dare a kauyukan Apyiashyim, Atak’mawai, Kibori da Kurmin Masara a masarautar Atyap.
Wata majiya ta bayyana cewa saboda ruwan saman da ake yi, ‘yan bindigan sun ci karansu ba babbaka duk da dokar ta bacin da gwamnatin ta sa.
Wani mazaunin kauyen Atak’mawai (Kurmin Masara), Irimiya Gandu, wanda ya tabbatar da harin ya ce rayuka akalla 12 sun salwanta yayin da aka kona gidaje da yawa.
Ya ce maharan sun dira unguwar misalin karfe 1 na dare yayin da al’umman kauyukan ke barci.
“Lokacin da na fara jin karar harbin bindiga na shiga gida na kwashi iyalaina muka boye wani waje. An kashe mutane 12, yawanci yara da mata.” Ya ce
Wani mazaunin Apiojyim da ke garin Kibori, Jonathan Ishaya, ya ce mutane bakwai aka kashe a daren yayin da aka kai musu hari.
A cewarsa, ‘yan bindigan sun dira kauyen ne misalin karfe 11 na dare kuma suka fara harbin kan mai uwa da wabi.
“Niyyarsu shi ne su kawo harin ba-zata, amma yayin da suka iso, sai suka isar da matasanmu na sintiri kuma suka yi musayar wuta.” Ya ce
“Mun birne mutane bakwai yau (Alhamis), har da dan shekara 80.” Ya kara.
Wata takardar da Kakakin kungiyar al’ummar kudancin Kadna SOKAPU, Luka Biniyat, ya saki ya ce jama’ar masarautar Atyap 33 aka kashe cikin kauyuka biyar: Apiojyim, Kibori, Apiako, Atakmawe da Magamiya.
Ya mika kokon barar kungiyar ga kasashen duniya a kawo musu dauki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here