An Sake Tsawaita Dokar Kullen Covid-19 Na Tsawon Makonni 4 A Najeriya

1
316
Daga Usman Nasidi.
SHUGABAN kasa, Muhammadu Buhari ya ba da izinin sake tsawaita kullen kasa baki daya har na tsawon makwanni hudu yayin da kasar ke ci gaba da gwagwarmayar kawar da cutar ta COVID-19.
Wannan shi ne karo na uku a cikin karni na biyu da gwamnatin ta ke kara kulle kasar bayan sassauta dokar kullen da zummar daukar matakan dakatar da yaduwar cutar a Yammacin Afirka.
A ranar Alhamis da yamma ne Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF) da kuma Shugaban Kungiyar Tattaunawa (PTF) kan COVID-19 Boss Mustapha ya ba da sanarwar daukar matakin a yayin wani taron da aka yi na Aiki a Abuja.
Kasar Najeriya na daya daga cikin kasashen da cutar Covid-19 ta fi kamari a Afirka, sakamakon akalla 44,890 da suka kamu da cutar kana aka mutuwar akallamutane 927.
Adadin kararraki da aka samu a kasashen Afirka ta Yamma, kasar na daya daga cikin kasashe uku masy mafi yawan a nahiyar, wanda kasar Afirka ta Kudu da Masar ne kawai suka hada su.

1 COMMENT

  1. a gaskiya yakamata a tausayawa talaka wlhi munacikin wani hali nadunci rayuwa babu aikin komai a nageria a halin yanxu

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here