Kwamitin Da Ke Bincike Kan Ibrahim Magu Na Iya Kammala Aiki Kwanan Nan

0
225
Daga Usman Nasidi.
A Makon nan da aka shiga ne ake tunanin cewa kwamitin da aka kafa domin ya binciki tsohon shugaban hukumar EFCC , Ibrahim Magu, zai kammala aikinsa.
Rahotanni sun bayyana cewa watakila wannan kwamiti da shugaban kasa ya ba alhakin gudanar da bincike a kan aikin EFCC, ya gabatar da sakamakon aikin da ya yi.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba wannan kwamiti na musamman tsawon kwanaki 45 ya karkare binciken zargin da ke kan wuyan tsohon shugaban hukumar EFCC.
A takardar da shugaban kasa ya sa hannu domin bada iznin binciken badakalar da ke kan Ibrahim Magu, ya nemi a duba duk ayyukan da EFCC ta yi tsakanin 2015 zuwa 2020.
‘Yan kwamitin sun hada da Ayo Salami a matsayin shugaba da kuma DIG Michael Ogbezi, Muhammad Babadoko (daga ma’aikatar shari’a) da Hassan Abdullahi (daga DSS).
Sauran ‘yan kwamitin su ne: Muhammad Shamsudeen (OAGF), Douglas Egweme (NFIU), sai kuma Kazeem Atitebi wanda shi ne sakataren kwamitin binciken.
Kwamitin ya kunshi wakilai daga kowane bangare na fadin kasar wanda su ka soma aiki a ranar 3 ga watan Yuli. Ana sa ran su gabatar da rahotonsu kafin ranar 19 ga watan Agustan 2020.
Idan abubuwa sun tafi daidai, a cikin makon nan shugaban kasa zai karbi rahoton aikin da aka yi. Kwamitin ya saurari ta-bakin jama’a, sai dai an yi wannan ne ba a bainar jama’a ba.
Ana binciken Magu da laifuffukan da su ka hada da rashin gaskiya, watsi da umarnin kotu . Sai kuma saida kadarorin da aka karbe daga hannun barayi, da bi ta kan dukiyar gwamnati.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here