An Yanke Wa Mawaƙi Hukuncin Kisa Bisa Yin Batanci Ga Annabi

0
334
Rabo Haladu Daga Kaduna
WATA babbar kotun Jihar Kano ta yanke wa wani matashi mai shekara 22 hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa yin kalaman ɓatanci ga Annabi Muhammad S.A.W. tare da wani da ya yi ɓatanci ga Allah.
Baba Jibo Ibrahim, Kakakin Babbar Kotun Kano, shi ne ya tabbatar wa da  manema labarai  hakan, inda ya ce dukkaninsu suna da damar ɗaukaka ƙara.
“An yanke wa matashin mai suna Yahaya Aminu Sharif hukuncin kisa ne sakamakon danganta Annabi S.A.W. da ya yi da shirka,” in ji Jibo Ibrahim.
“A halin yanzu za a rataye shi har sai ya mutu, kamar yadda sashe na 382 (b) na kundin tsarin mulik na shekarar 2000 yatanada.
Tun a watan Maris na 2020 ne Aminu Sharif, mazaunin unguwar Sharifai da ke ƙwaryar birnin Kano ya yi wata waƙa, wadda aka zarge shi da yin ɓatancin a cikinta.
Kazalika kotun ta yanke wa wani matashin mai suna Umar Farouq hukuncin shekara 10 a gidan yari tare da horo mai tsanani bisa laifin ɓatanci ga Allah Maɗaukakin Sarki.
Alƙali ya yanke wa Umar Farouq hukuncin ne sakamakon shekarunsa ba su kai 18 kamar yadda kundin manyan laifuka ya tanada.
Ya yi ɓatancin ne yayin da suke yin ce-ku-ce da wani

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here