Za Mu Yi Aiki Sosai Domin Bunkasa Kasuwar Dawanau-Inji Sani Ahmed Kwa.

0
445
Daga Jabiru Hassan.

SHUGABAN kwamitin rikon Kasuwar kayan abinci ta duniya Alhaji Sani Ahmed Kwa yace kwamitin da aka nada domin tafiyar da harkokin Kasuwar zai yi aiki sosai domin ganin an sami ci gaba mai kyau ta fuskar cinikayya da tattalin arziki.

Yayi wannan tsokaci ne yayin da wakilin muya ziyarci ofishin Kasuwar, inda ya bayyana cewa da yardar Ubangiji, zasu yi kokari wajen kawo managarcin ci gaba ta fuskar kasuwancin kayan amfanin gona da kuma kyautata dangantaka tsakanin yan Kasuwar da kuma masu fataucin kayan abinci daga wasu sassa na duniya.

Alhaji Sani Ahmed Kwa ya kuma nunar da cewa an kafa wannan kwamiti masu ne domin ya tafiyar da kasuwar tareda hade kan yan Kasuwar da kuma shirya zaben shugabannin da zasu jagoranci Kasuwar ta Dawanau a tsari irin na dimokuradiyyar kungiyar yan kasuwa.

Yayi godiya  ga shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa Alhaji Ado Tambai  Kwa a madadin sauran yan kwamitin rikon saboda damar da ya basu na bada gudummawa wajen bunkasa kaauwar Dawanau kamar yadda ake gani a yanzu.

Kwamitin  yana da Alhaji Sani Ahmed Kwa a matsayin shugaba sai sauran yan kwamitin da suka hada da Alhaji Usman Yahaya Dawakin Tofa da Alhaji Baliya Alasan Dawanau da wakilin Hakimi Alhaji Tsoho Rabiu da Alhaji Kabiru Idris Tsanyawa da Alhaji Mu'azu Aliyu.

Sauran yan kwamitin sun hada da Alhaji Jamilu Alhassan Dawanau da Alhaji hamisu Sarkin kaauwa da Alhaji Kabiru Aminu da I.S.Binger da Alhaji Murtala Ibrahim Yusuf da Mustapha Rabiu P.A  yayin da Alhaji Bashir Musa ya kasance sakataren kwamitin na kaauwar Dawanau.
Gaskiya Tafi Kwabo  ta sami zantawa da wasu daga cikin yan kaauwar ta Dawanau inda suka bayyana cewa wannan kwamitin riko zai kawo ci gaba a kasuwar musamman ganin yadda aka zakulo mutanen da suke jagorantar kwamitin da yadda suka fara aikin tafiyar da sauye-sauye a wannan kasuwa mai tsohon tarihi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here