An Zabi Shugabannin NUJ Na Rediyon Aminci A Kano

0
259

Mustapha Imrana Abdullahi

A kokarin ganin an tafiyar da ayyukan manema labarai kamar yadda ya dace kungiyar ‘yan jarida reshen Gidan rediyon Aminci da ke Kano sun zabi sababbin shugabanni karkashin jagorancin Kwamared Aliyu Sufyan.

Kwamared Aliyu Sufyan wanda ya kasance Edita ne kuma shugaban wani shirin siyasa da ake gabatarwa a gidan rediyon ya dauki rantsuwar yin shugabancin kungiyar NUJ reshen gidan rediyon tare da sauran jama’a kamar haka.

Akwai mataimakin shugaba, Ummushakeer Ahmed, sakatare, Abubakar Haruna Galadanci, sakataren kudi,Sa’adatu Hussain Ya’u, Ma’ajin kungiyar, Shamsudden Mustapha Danhaki, Mai binciken kudi,  Garzali Jibril Maimashi Bebeji, sai kuma babban mai bincike, Shazali Farawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here