Kungiyar Makafi Ta Bukaci Gwamnatin Kaduna Da Ta Sako Mutane 140 Da Aka Kama

0
265

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

KUNGIYAR Makafi da ke Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta saki membobin kungiyar su dari da arba’in da aka kama a kan tituna.

Jami’in hulda da jama’a na kungiyar, Mallam Sadiku Ahmad ne ya sanar da hakan yayin da yake yi wa manema labarai karin haske a sakatariyar kungiyar ‘yan Jaridu ta Najeriya, rashen jihar Kaduna.

Ya bayyana cewa jami’an tsaron sun kama mambobin nasu ne sannan suka kai su sansanin aikin hajji da ke Mando a karamar hukumar lgabi ta jihar Kaduna.

A cewarsa, Jami’an tsaro a jihar sun kori mutanensu fiye da mutane dari takwas da suke nakasassu da ke cikin jihar.

Ya ce “Gwamnatin jihar Kaduna ta dauki matakin daukar matakin saboda ba wai kawai an cutar da mambobinmu ba, har ma suna tilasta wa mutanen mu ficewa daga cikin gidajen su ta hanyar yin amfani da jami’an tsaro da bindigogi.”

A cewarsa, wasu daga cikin shuwagabannin nasu sun yi bayanin cewa asalinsu ‘yan asalin jihar ne.

“Muna zaune a cikin jihar Kaduna tun shekaru 30 zuwa 40 da suka gabata. Wasu shuwagabannin siyasa da wasunsu masu rike da mukaman siyasa an haife su ne a gaban idanunmu, don haka mu ‘yan asalin jihar nan ne.”

“Ba mu da sauran wuraren da za mu je kuma abin takaici ne cewa gwamnati ta fitar da mu daga gidajenmu ba tare da samar mana da wani madadinmu ba,” inji su.

Kungiyar ta yi kira ga gwamnati da ta zama mai tausayi, tare kuma da samar musu da abubuwan more rayuwa da wurin zama.

A cewarsu sana’ar bara ba harkar kasuwanci ba ne, ya kara da cewa ba suna nan ne saboda suna son hakan ba amma illa saboda yanayin da suka tsinci kansu, don haka ya yi kira ga gwamnati da ta samar musu da wani wajen koyon sana’a don su samu damar biyan bukatun kansu da nasu iyalen.

Da yake magana da Kwamishinan Ayyuka da ci gaban Al’umma Hafsat Mohammed Baba ya yi gargadin cewa tuni jihar ta hana yin bara a tituna kuma duk wanda aka samu a kan titi yana yi za a kama shi.

Ta ci gaba da cewa mabaratan sun lalata wurin zaman da Gwamnatin ta basu ta hanyar yin amfani da shi ba yadda ya kamata ba shi ba yadda za ta yi illa ta tashe su tare da rushe wajen.

Hajiya Hafsat Baba ta bayyana cewa marokan sun ba da gudummawarsu wajen ba da kulawa ga cutar da kananan yara da lalata muhallinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here