NHR Za Ta Ci Gaba Da Kare Hakkin Al’uma Tare Da Inganta Bin Dokoki-Ayagi.

0
290
Jabiru A Hassan, Daga Kano.
BABBAN daraktan kungiyar kare hakkin dan Adam ta “Human Rights Network” Kwamared A.A.Haruna Ayagi ya ce kungiyar za ta ci gaba da aiki dare da rana domin kare hakkin al’uma tare da tabbatar da ganin ana bin dokokin kasa cikin nasara.
Ya yi wannan bayani ne a hirar su da wakilinmu a ofishin kungiyar, tareda sanar da cewa mafiya yawan lokuta al’uma suna shiga cikin yanayi na bukatar taimako wanda sune suke shiga cikin lamarin har a sami masalaha  kamar yadda ake gani kullum.
Kwamared Ayagi ya yi bayanin cewa kungiyar su ta HRN tana da kyakykyawar dangantaka da dukkanin hukumomin tsaro da ke kasarnan, sannan tana kuma da alaka ta aiki tsakanin ta da kungiyar Rabin kare hakkin dan Adam ta duniya watau Human Rights Watch domin tabbatar da ganin komai yana tafiya cikin nasara.
Babban daraktan kungiyar ta HRN ya kara da cewa suna aiki da dukkanin kafafen yada labarai na cikin da wajen kasar nan, sannan suna sanya ayyukansu a cikin kafafen sadarwa na zamani da ake kira social media ta yadda al’uma zasu fahimci yadda aikace-aikacen su ke tafiya.
Daga nan sai ya nunar da cewa kofar su a bude take ga dukkanin wanda take ganin an yi masa ba daidai ba walau a hukumance ko kuma tsakaninsa da wani ko wasu da suka nuna masa fin karfi domin ganin an kwato masa hakkin da cikin tsarin aikin kungiyar.
Kwamared A.A.Haruna Ayagi  ya bayyana cewa kungiyar tana aiki ne bisa izinin dukkanin hukumomin tsaron kasa, kana tana bibiyar dukkanin korafe-korafen da al’uma suka gabatar gare su don tabbatar da cewa komai yana tafiya daidai, tare da fatan cewa mutane za su kara fahimtar su kamar yadda ya kamata.
A karshe, babban daraktan ya yi godiya ta musamman ga rundunar ‘yan sandan Nijeriya da hukumomin shari’a da na lura da shige da fice da na sauraron korafe-korafen al’uma da kuma su kansu al”umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here