Daliban Najeriya Sun Bayyana Ranar Da Za Su Yi Zanga-Zanga A NASS

0
194

Daga Usman Nasidi.

DALIBAN jami’o’i karkashin inuwar kungiyar daliban jami’o’i ta kasa ta ce hakurinsu ya kare sakamakon dogon yajin aikin da kungiyar malamai masu koyarwa na jami’o’i suka fada.

Daliban sun ce za su nuna rashin jin dadinsu a kan yadda yajin aikin ke tsawaita a ranar Talata.

Sun ce za su fara zanga-zangar ne ta gaban katafaren ginin majalisar tarayya sannan su wuce zuwa ofishin ma’aikatar ilimi daga nan su garzarya zuwa ma’aikatar kwadago da aikin yi.

A wasikar da suka fitar a ranar 13 ga watan Oktoban 2020 wacce suka mika ga majalaisar, kungiyar da ta hada da shugabanninta daga dukkan jami’o’i, ta ce dalibai sun zaunu a gida kuma suna bukatar a janye yajin aikin da gaggawa.

Wasikar ta samu sa hannun shugaban NAUS Ibrahim Lawal, mataimakinsa, Asiwaju Ajibowu da magatakarda, Gbande Abraham.

A yayin zantawa da manema labarai a kan zanga-zangar da ke zuwa, Lawal ya ce gwamnatin ta gaza kuma ya zama dole su yi abinda ya dace saboda tsawaitar yajin aikin.

Ya ce, “Muna gayyatar dukkan dalibai da su fito domin zanga-zanga saboda mun gaji da zaman gida kuma ilimi yana da matukar amfani.

“A watan Augusta, mun rubuta wasika ga ministan ilimi a kan bude makarantu. Mun bakacesa da ya kawo karashe yajin aikin ASUU. “Amma kuma ministan bai yi martani a kan wasikar ba. Mun yi iyakar hakurin da za mu iya amma bamu ji daga minsitan ba. Mun gaji.”

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here