Yan Arewa Mazauna Orlu Na Barin Garin Sakamakon Hari Da Aka Kai Musu

0
219

Musa Muhammad Kutama Daga Kalaba.

TUN bayan harin ta’adancin da kungiyar sakai ta tsaro yankin kudu maso Gabas ta Kaiwa ‘Yan Arewa mazauna garin Orlu dake Jihar Imo a Karamar hukumar Njaba, Al’ummar Arewa na tattare komatsen su suna komawa garurukan su na asali.

Shugaban matasan ‘yan Arewa mazauna Orlu Alhaji Amadu Ali ne ya shaidawa wakilin mu na kudanci  haka inda bayyana cewa halin da suke ciki shi ne ‘Yan Arewa na bin hanyoyi na ‘badda-kama da zasu sulale zuwa garuruwansu inda suka fito.

Ya ce “a halin yanzu muna cikin ha’ula’i yanzu babu halin da indai kai dan Arewa ne da za ace ka fita kayi sana’a domin ‘yan island suna bi suna dubawa suga wanda ya rage su kai masa hari yasa kowa na boyewa a masaukin sa don nima yanzu haka zancen nan da nake yi da kai Ina kan hanyar ta tafiya arewa.” Inji shi

Ya ci gaba da cewa da wuya kaga bahaushe yanzu a Orlu domin suna ta tafiya gida wasu Kuma sun nemi mafaka a wasu garurukan kafin suma su tafi gida.

Ya bayyana sunayen mutane biyu da aka kashe a matsayin Muhammadu dan sarkin Hausawa Orlu da Sani Ma’azu kana ya ce sauran wadanda aka kashe a wata Karamar hukuma ce mai Suna Njaba.

 

 

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here