Akalla Sama Da Mutane 60 ‘Yan Arewa Mazauna Imo Suka Bar Gari

0
274

Musa Muhammad Kutama, Daga Kalaba.

Fargabar kara ci gaba da kai musu Hare-haren ta’addanci a wuraren sanao’in su, wasu ‘Yan Arewa mazauna Jihar Imo na ci gaba da tattara ‘Yan komatsen su suna ficewa daga jihar.

Makon da ya gabata ne wasu ‘Yan ta’adda suka Kaiwa ‘yan Arewa mazauna garin Orlu da kauyen Omaka hari suka kashe mutum bakwai da narkar dukiya wanda asarar rayuwa da aka yi musu babu wani mataki kwakkwara da aka dauka na hana ci gaban faruwar hakan da alamun kara kawo musu Wani harin wanda hakan yasa su zaman zullumi da Kuma kunci na rayuwa .

Masu barin jihar kamar yadda wannan jarida ta ruwaito labarin cewa yawanci su sun fito daga Jihohin kano, katsina da Kuma sokoto.

Mutune sama da sattin ne aka kiyasta suka bar jihar tun daga ranar Lahadi makon da ya gabata suke yi ficewarsu daga garin Owerri hedkwatar jihar, hakazalika mazauna kauyen Omaka da Orlu Yan Arewar tuni suka bar musu garurukan bayan wancan harin da aka kashe mutum bakwai.

Alhaji Dan Asabe Umar Wani mazaunin Garin Owerri dake gudanar da harkokin kasuwancin sa ya shaidawa wakilin mu na kudanci cewa haka siddan suke zuwa a kan babura Suna bude musu wuta alhali babu wani fada ko bakar magana ko rigima data hada su dasu suke kashe su

Ya ci gaba da cewa ya zuwa yanzu “sama da mutum 60 ne suka tafi gida sokoto, sauran Jihohin a lissafin mutanen da suka tafi Yan jihar kano da katsina ne wanda a lokacin da ake hira nan dashi bankwana suke yi don sh ima Arewa zai tafi.

Haka nan kuma domin Jin halin da sauran Al’ummar Arewa mazauna unguwar Hausawa dake Owerri da aka fi sani da Oma Hausa, Alhaji Jibrin Babangida ya shaidawa wakilin mu cewa tsare oma Hausa kadai da jami’an tsaro suka Yi da gwamnati ta turo hakan ba zai wadatar da su ba domin akwai sauran yankunan da Hausawa suke ba don komai ba sai domin suna yawon tallar Aya ko yankin farce da Kuma aikin wanke takalmi don Kada a rika bin su ana musu kisan mummuke baya ga masu sana’ar neman karafa da aka yar a juji.

Dangane da halin da ake ciki yanzu, Alhaji Babangida ya ci gaba da bayanin halin da suke ciki ya ce “Gaskiya muna cikin Wani irin Hali mawuyacin gaske, muna ci gaba da zaman Dar-dar ne. ”

Karin Hari da Yan ta’adda suka kai a Baya suka kona Wani ofishin  Yan sandan jihar Imo da Kuma fasa gidan yarin gyara halin inda suka kubutar da wasu wanda hakan ya kara jefa Yan arewar cikin firgici kuma ya taimakawa matuka wajen rashin samun cikakkiyar natsuwa ta ko  gwamnati zata iya basu cikakkiyar kariya da Kuma tsaro.

Wakilin mu ya yi kokarin jin tabakin kwamishinan Yan sandan jihar Haruna Mohammed, amma abin yaci tura.

Masana kan harkokin tsaro na ganin cewa idan matukar gwamnati dagaske take yi na shawo kan matsalar tsaro a kasar nan, to wajibi ne ta shigo da kungiyoyin fararen hula domin zasu fi kowa jin labarin halin da ake ciki, Kuma inyaso su sanarwa hukuma ta dauki matakin da ya dace “Amma yanzu kowa ce gaba ta tsaro idan ta samu nata bayanan sirri ba zata bajewa takwarat ta ba domin a hadu ayi aiki tare domin samun Nasara “

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here