An Tsinci Gawarwakin Mutane 15 A Magudanar Ruwa A Garin Kalaba

0
270

Musa Muhammad Kutama, Daga Kalaba.

AL’UMMAR dake unguwar mil 5 dake yankin Karamar hukumar Birnin Kalaba a ranar Talata sun wayi gari cikin firgici da dimauta bayan da suka ga gawar mutum 15 maza da mata da aka watsar a magudanar ruwa dake kan Babbar hanyar shiga Garin Kalaba.

Ganin kudaje na karakaina kan gawarwakin ne ya sanya mutanen unguwar suka je suga me ke faruwa inda suka iske gawarwakin. Ana kyautata zato wata Kila anyi fada ne a Wani wurin aka kwaso gawarwakin aka jibge a lambatu.

Uwem Ekarika Wani mazaunin unguwar ya shaidawa wakilin cewa “Da safiyar Talata ce suka ga kudaje na yawo a wurin Sai wari da hamami ke tashi shi ne aka je aka ga ashe gawarwakin mutane ne aka yasar a wajen.

Sai dai babu tabbacin ko suwaye suka kawo gawarwakin amma wata majiyar ta shaidawa wakilin mu cewa “Anji alamun mota ta tsaya wurin da talatainin dare amma babu tabbas ko daga Ina aka kawo gawarwakin.

Wakilin mu na kudanci ya  tuntubi Dsp Irene Ugbo mai magana da yawun rundunar Yan sandan kuros riba amma Bata amsa waya ba. Ya zuwa rubuta wannan labari dukkan nin kokarin Jin ta bakin mahukuntan yaci tura domin hatta kwamishinan Yan sandan Jihar kuros Riba Sikiru Akande ya yi gum da bakinsa game da lamarin.

 

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here