Kwalejin Fasha Ta Bichi Ta  Ciri Tuta

  0
  349
  JABIRU A HASSAN, Daga Kano.
  A DUK lokacin da aka yi maganar harkar ilimi, a kan yi waiwaye kan wasu muhimman batutuwa dake zamewa barazana ga yanayin koyo da koyarwa musamman a wannan lokaci da ake ciki na kalubalen tattalin arziki a duniya baki daya duba da yadda annobar cutar Korona ta yi illoli ga kowane irin lamari.
  Sannan kowa ya fahimci cewa harkar ilimi tana bukatar hada hannu tsakanin gwamnatoci da kungiyoyin iyayen yara da malamai da kuma kwamitocin gudanar da shugabancin ilimi ta yadda kwalliya zata ci gaba da biyan kudin sabulu wanda hakan ta sanya al’amura ke tafiya cikin nasara.

  Bisa wadannan misalai, nake amfani da wannan dama wajen bayyana irin kokarin da mahukumtan kwalejin fasaha ta tarayya dake Bichi watau “Federal College Of Education (Technical) Bichi bisa jagoranchin  Shugaban kwalejin Farfesa Bashir Muhammad Fagge da mataimakan sa.

  Sanin kowa ne cewa akwai ire-iren wadannan kwalejoji na gwamnatin tarayya dake ko’ina a kasarnan domin tabbatar da ganin ana bada ingantaccen horo kan ilimin fasaha ta yadda duniya zata rabauta da kwararru ta kowane fanni na zamantakewar dan Adam.
  Haka kuma ina mai jinjinawa Farfesa Bashir Fagge saboda tsayawa kan gaskiya da yake yi wajen tabbatar da cewa kwalejin fasaha ta Bichi ta ci gaba da rike kambun ta na makaranta mafi wanzuwa kan manhajar da aka amince da it’s wajen tafiyar da harkokin bada horo da kuma tarbiyya.
  Duk Wanda ya sami damar ziyartar wannan kwaleji zai amince cewa ana samun ci gaba mai kyau a gurin tareda ci gaba da samarda yanayin koyo da koyarwa mai gamsarwa duba da yadda makarantar ta yi fice kan samarda managartan dalubai wadanda a yau dinnan suka kasance abin alfahari ga kasa da kuma duniya.
  Sai dai wani abin rashin jin dadi shine yadda aka sami wasu daga cikin malamai visa doron kungiyar su ta malaman kwalejojin fasaha reshen makarantar suna kushe dukkanin kokarin da mahukumtan kwalejin keyi bisa jagorancin Farfesa Bashir Muhammad Fagge watakila domin wata biyan bukata tasu.
  Wannan korafi da wadannan malamai suka gabatar ya sanya shakku a zukatan wadanda suke ziyartar kwalejin domin gudanar da wasu harkoki da suka shafi ilimi ko aiyukan yau da kullum, sannan an hakikance cewa kwalejin fasaha ta gwamnatin tarayya dake Bichi ta ciri tuta ta fuskar bada ilimi mai nagarta da kula da tarbiyyar dalubai maza da mata.
  A karshe,  tarihin shugabancin  kwalejin fasaha ta Bichi bazai man da Farfesa Bashir Muhammad Fagge ba saboda kokarin da yake yi wajen kare mastaba da darajar kwalejin duk kuwa da irin kalubalen da yake fuskanta na karancin kudade na gudanar da aiyuka a kowane fanni sakamakon halin da duniya ta shiga.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here